Gwamnan jihar Neja Sani Bello ya bayyana cewa akalla mutum 220 ne aka kashe a kauyuka 300 daga ranar daya zuwa 17 ga Janairun 2022 a jihar.
Bello ya fadi haka wa manema labarai bayan ya ganawa da yayi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Abuja.
“A tsakanin wannan lokaci gwamnati ta samu rahotannin hare-haren ‘yan bindiga 50 daga kauyuka 300 a jihar.
“An yi garkuwa da mutum 200 inda a ciki akwai ‘yan kasan Chana uku, an kashe masu gadi 25 sannan an kashe farin hula 165 da ‘yan kungiyar sa kai 30.
Bello ya ce baya ga jihar Neja ‘yan bindigan na kai wa jihohin dake kusa da su hari.
“Idan muka fafure su muka bude wa maharan wuta sai su koma jihar Kaduna idan a can ma aka fatattake su sai su koma jihar Katsina.
“Abin da ya kamata a yi shine a hada hannu domin ganin bayan wadannan mahara.
Bello ya ce gwamnati za ta saka tsauraran matakai domin ganin an kawo karshen ‘yan bindiga a jihar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya shugaban ƙasa Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu tsauraran matakan da za su taimaka wajen kawo karshen ‘yan bindiga a jihar Neja.
Har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da maida hankali wajen ganin an kawo matsalar rashin tsaro a musamman yankin Arewa.