Shugaban jami’ar Maryam Abacha dake Kano Farfesa Abubakar Gwarzo ya kaddamar da sabon titi a cikin jami’ar da aka naɗa wa sunan marigayiya Haneefa Abdussalam.
Farfesa Gwarzo tare da mahaifin marigayiya Haneefa suka kaddamar da wannan titi ranar Lahadi a wata gajeruwar biki.
Farfesa Gwarzo ya ce jami’ar ta yi haka ne domin a karrama marigayiya Haneefa da ta rasa ranta ta hanyar kisa da wani malaminta ya yi.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda shugaban makarantan da Haneefa ke karatu ya sace sannan bayan iyayenta sun biya kaɗan daga cikin kuɗin fansa ya kashe ta ya kuma birne ta a wani ɓangaren makarantar sa.
Wannan mummunar abu da malamin yayi ya tada wa ƴan Najeriya da dama hankali inda aka yi masa tofin Alla-tsine kan abinda ya aikata.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyayen marigayiya Haneefa.
Haka kuma shima ministan Sadarwa, Farfesa Ali Pantami ya kai ziyara har gidan iyayen wannan baiwar Allah da aka kashi bata ji ba bata gani ba.
Wasu da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA game da wannan abu da jami’ar Maryam Abacha ta yi sun yaba wa mahuntan wannan makaranta bisa hangen nesa da suka suka raɗa wa wani titi a cikin jami’ar sunan marigayiyar.