Hatsarin mota a yau Litinin yayi sanadiyar mutuwar Yan kasuwa daga Gaya, Jihar Kano su tara akan hanyarsu ta zuwa kasuwar Shuwarin dake Karamar Hukumar Kiyawa, Jihar Jigawa.
Hatsarin ya auku ne a daidai kauyukan Sabaru da Labara akan Babban titin Kano zuwa Maiduguri.
Kakakin Hukumar Kiyaye hatsari na kasa, reshen Jihar Jigawa, Ibrahim Gambo, ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa ma’aikatansu na ceto sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa kuma sun Kai wadanda suka ji rauni asabiti.
Motocin da hatsarin ya ritsa dasu sun hada da Tayota Huma bas Mai lamba DRZ 846, XA da Sharan Mai Lamba Dal, 830, XA.
Kakakin yace motocin sunyi tahu mu gama da juna a lokacinda daya dake cikinsu yayi kokarin kauce wa Rami.
Yace mutum sha Tara ne a cikin motar, Maza 17 da Mata 2 amma duk mazan ne suka mutu.
Mai Taimakawa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, Kan Sababbin Kafafen Yada Labarai, Bashir Ahmad, a shafinsa na Facebook, yace hatsarin “ya rutsa da wasu ‘yan kasuwar Gaya a hanyar su ta zuwa wajen kasuwancin su.
“Hatsarin yayi sanadiyyar rasuwar da dama daga cikin ‘yan kasuwan wadanda dukkan su suna da matukar muhimmanci ga garin Gaya da mutanen ta.
“Ina mika sakon ta’aziyya ga Mai Girma Sarkin Gaya, Aliyu Gaya, Mai Girma, Shugaban Karamar Hukumar Gaya, Hon. Ahmad A. Tashi, ‘yan uwan wadanda hatsarin ya shafa da sauran mutanen gari.
“Ina rokon Allah ya jikan su, ya kuma ba mu hakurin jure wannan babban rashin, sannan Allah ya kiyaye faruwar irin hakan anan gaba, cewar Kakakin na shugaba Buhari.