Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ƙara wa lemun zaƙi harajin kashi 10%, lamarin da zai tilasta tsadar lemun kwalba, na gwangwani da na kwali a ƙasar nan.
Ministar Harakokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a ranar Juma’a a Abuja, yayin da ta ke gabatar wa jama’a filla-fillar kasafin 2023.
Ta ce harajin da za a ɗora wa kayan zaƙi na cikin Sabuwar Dokar Kuɗaɗe ta 2021, wadda za ta fara aiki a cikin Janairu 2022 da muke ciki.
Sannan kuma ta ce an yi wannan hoɓbasan ne domin ƙara samun kuɗin shiga ga gwamnati.
Zainab ta ce Gwamnatin Tarayya ta ƙirƙiro wannan sabon harajin ne bisa bin umarnin Bankin Duniya da Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Waɗanda su ka shawarci Najeriya ta ƙara fito da hanyoyin samun kuɗin shiga a cikin gida.
A gefe ɗaya kuma ta ce za a ƙara sa ido sosai kan kamfanonin da ke ƙarƙashin gwamnati, domin su tabbatar su na tara harajin da aka gindiya masu su riƙa tarawa.
A kan haka ne ma ta ce za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗɗan tara kuɗaɗen shigar da aka umarci ya tara.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton cewa 2022 za ta kasance shekarar da tsadar fetur da harajin jiki magayi za su yi wa ‘yan Najeriya lilis.
A ƙarshen 2021 Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta jefa ‘yan Najeriya cikin tunanin irin mawuyacin halin da za a shiga a shekarar 2022.
Yayin da Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa a cikin 2022 za a bijiro da sabbin hanyoyin tatsar kuɗaɗen haraji a ƙasar nan, a ɓangaren man fetur kuma gwamnati cewa ta yi za ta cire tallafi.
Idan an cire tallafin kuwa, da kan ta cewa ta yi farashin litar mai za ta iya kaiwa naira 340.
Tsarabar 2022: Gwamnatin Buhari Za Ta Tsula Farashin Litar Fetur, Amma Za A Riƙa Biyan Talakawa Naira 5000 Su Rage Raɗadin Ƙuncin Rayuwa
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta cire kuɗin tallafin man fetur, wanda hakan na nufin za a ƙara kuɗin litar fetur.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a lokacin ƙaddamar da wani shiri na Bankin Duniya a Najeriya.
Sai dai kuma ta ce gwamnatin tarayya za ta zaƙulo mutane miliyan 30 zuwa 40 da su ka fi kowa talauci a kasar nan ta riƙa ba su naira 5,000 kowace Wata, domin rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su iya afkawa a ciki nan gaba idan an ƙara wa fetur farashi.
Ta ce rarar kuɗaɗen da za a riƙa samu ce za a duba sannan a san ko adadin mutum nawa ne za su riƙa amfana da tallafin.
Idan ba a manta ba, Bankin Bada Lamuni na Duniya, IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin mai domin ta ƙara samun kuɗin shiga. Kuma ta rage kashe kuɗaɗe a ayyukan da ba masu muhimmanci ba.
Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin da na kuɗin wutar lantarki a farkon 2022:
Idan Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da shawarar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) har ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki a farkon 2022, ‘yan ƙasar nan za su shiga sabuwar shekara cikin halin ƙuncin rayuwar da ta fi ta shekarar 2021 da ake ciki.
Kai tsaye ba wani abu ba ne cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, ma’ana ita ce a ƙara wa farashin litar man fetur da wutar lantarki kuɗi.
IMF ta gargaɗi Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021, to haka ma za ta kasance a shekara mai zuwa.