Idan ka ɗebe Atiku Abubakar, wanda har Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi tsawon shekaru takwas, babu wanda ya kai Bola Ahmed TInubu daɗewa da goyayyar rugumutsin siyasa da gwajingwalimar da ke tattare da mulkin dimokraɗiyya.
Kuma banda Atiku babu wanda ya kai Tinubu daɗewa a fagen siyasar ana tsalle ana direwa da shi ko ba da shi.
Hasali ma su Tinubu ne tantiran ‘yan NADECO, ƙungiyar da ta riƙa tsone wa sojoji ido, har su ka haƙura suka bayar da mulki cikin 1999.
A sani cewa Tinubu ya yi gudun famfalaƙi zuwa ƙasar Ingila, inda ya ɓoye saboda kauce wa fushin shugaban mulkin soja na lokacin, marigayi Janar Sani Abacha, kuma ya shafe shekaru a Landan, ba ma shekara ɗaya ba.
Rigimar Tinubu Da Obasanjo: Kyan Faɗa A Kwana Ana Yi:
Bayan sojoji sun bayar da mulki ga farar hula, Obasanjo ya fito daga kukukun Gashuwa a Jihar Yobe, ya zama shugaban ƙasa a 2999. Shi kuma Tinubu ya dawo daga gudun hijira, ya ajiye NAAECOnci gefe, ya zama Gwamnan Jihar Legas, shi ma a 1999.
Yayin da aka kammala zango na ɗaya, Obasanjo ya zarce, shi ma Tinubu ya zarce. Sai dai kuma su biyun sun zarce cikin wawakeken ramin da su ka shafe watanni 17 su na turnuƙun rikici.
Asalin rikicin su kuwa shi ne wasu jihohi sun ƙirƙiro Ƙananan Hukumomi, waɗanda Gwamnatin Obasanjo ta ce sun keta dokar ƙasa.
An samu saɓani sosai, har ta kai Obasanjo ya ce duk wani gwamnan da bai soke waɗanda ya ƙirƙiro ba, to za a riƙe masa kuɗaɗen kason jihar waɗanda gwamnatin tarayya ke ba su.
Jin haka sai kowace jiha ta soke waɗanda ta ƙirƙiro ɗin, ta bar na da can. Amma jihar Legas kuwa, ya ce Obasanjo ya yi kaɗan.
Abu kamar wasa, Tinubu dai ya rigaya ya ƙara ƙananan hukumomin Legas daga 20, ya ƙara 37, wato sun koma 57 kenan.
Shi kuma Obasanjo ya sakar wa kowace jiha kuɗaɗen ta na ƙarshen wata, in banda jihar Legas.
Abu kamar wasa, tun daga watan Afrilu na 2004 har aka kai wata biyar, kowane wata ba a bai wa Jihar Legas ko sisi.
Daga wata biyar sai da aka kai watanni 17 ana kwamtsa shari’a tsakanin Tinubu da Obasanjo.
Cikin waɗancan watanni 17, Tinubu ya riƙa cuɗa guna da manta, wato ya riƙe Jihar Legas da kuɗaɗen shigar da jihar ke samu, ba tare da karɓar ko sisi daga Gwamnatin Tarayya ba.
Wata rana Obasanjo na Shuagaban Kasa, sai Tinubu ya je Fadar Shugaban Ƙasa, lokacin ya na gwamna, kuma ya na tsakiyar rikici da Obasanjon.
“Ina shiga wurin Obasanjo sai ya ce min fita ka ba ni wuri, ya za ka kai ni ƙara kuma ka zo ka na son gani na.” Inji Tinubu, cikin 2015, lokacin da ya ke bada labarin kwatagwangwamar sa da Obasanjo.
“Na ce masa, Baba wannan fadar fa ba taka ba ce, zaman haya ka ke yi, wata rana fita za ka yi. Ni ba kai na zo gani ba, aikin ‘yan jiha ta na kawo maka ka duba mu tattauna. Obasanjo ya ce min gaskiyar ka fa. To shigo ka zauna.”
“Wata rana kuma muka haɗu na ce masa ‘Baba na’. Ya ce ba baban ka ba ne, ba ɗan uwan ka ba ne, kuma ba abokin ka ba ne, tunda ka kai ni ƙara. Na ce masa ai ba Baba na kai ƙara ba. Ni Shugaban Najeriya na kai ƙara.”
Irin juriyar da Tinubu ya yi ya na faɗa da Obasanjo da yadda ya gyara Legas da bunƙasa tattalin arzikin ta, ya cancanci a kira shi ‘goga ka san hanyar jagoranci’.
Tinubu 2023: Inda Jagaba Ya Ɓata Rawar Sa Da Tsalle:
A halin yanzu Tinubu ba zai rasa yin da-na-sanin wasu kalamai da ya yi ba a kan Najeriya, a zamanin mulkin soja, lokacin da kan sa ke zafin aƙidar NADECO.
Wakilin jaridar Thisday mai suna Ayo Arowolo ya yi hira da Tinubu a lokacin da ya ke zaman gudun-hijira, a gidan sa na Landan, cikin 1997. A lokacin ya shafe shekaru biyu da tserewa Landan.
Thisday ta buga tattaunawar a ranar 11 Ga Afrilu, 1997, inda Tinubu ya ke cewa: “Ni ban yi imani da Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya ba.”
A yanzu da Jagaban ya taso ya na neman zama shugaban ƙasa, an fara bankaɗo shafukan wannan jarida ana yamaɗiɗi da su.
Sannan kuma Tinubu zai fuskanci ƙalubalen abin da ya tafka a jajibirin zaɓen 2019, inda a matsayin sa na jagoran jam’iyya mai mulki, ya lodo motoci biyu da kuɗi daga banki su ka kai masa har gida.
Har yanzu wanann abu ya zubar da kima da karsashin wannan gwamnati, wadda a lokacin ta riƙa bin ‘yan adawa ta na kamawa, amma ta ƙyale Tinubu ya yi
yadda ya ga dama da nasa kuɗin a lokacin zaɓe.
Yawan shekarun Tinubu za su ƙara kawo masa cikas, ganin cewa a lokacin da zai hau mulki idan ma ya samu takara ya ci zaɓe, to ya haura shekaru 70.
Duk da cewa ya taka rawar gani a zaɓen 2015, ana ganin bai dace ya nemi shugabanci ba, gara ya haƙura ya bar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Sai dai kuma zai yi wahala, domin Tinubu dai da gaske ya ke yi, kuma tallar sa tuni ta yi nisa.
Amma ko za a sake zaɓen tsoho kamar Tinubu? Ko za a zaɓi mutumin da ya taɓa cewa bai yi amanna da ci gaban Najeriya kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya ba?
Ko za a zaɓi wanda ya yi amanna da cewa kuɗi za su iya biya masa buƙata a ranar zaɓe?
Kuma ko za a amince a tsayar da shi takarar ma tukunna a ƙarƙashin APC?
Idan ana maganar mutane dai kam, TInubu na da jama’a a cikin gwamnati da kuma manyan ƙasa. Ya kafa gwamnoni kuma ya kafa ministoci.
To amma kuma su ma dukkan waɗanda za su iya taɗiye shi ya faɗi, a cikin gwamnatin su ke, sai kuma wasu dakkan ƙasar nan, waɗanda a gefe su ke, mayu ne na dauri, waɗanda sun ci dubu sai ceto. Amma ba za su ceci Tinubu ba!