Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantar da wani malami mai suna Abdulmalik Tanko ya kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar.
Kwamishinan ilimin jihar Muhammad Kiru ya sanar da haka a wata takarda da kakakinsa Aliyu Yusuf ya raba wa manema labarai ranar Juma’a.
Kwamishinan limin ya ce gwamnati ta soke lasisin aikin wannan makaranta da wasu makarantu biyu da aka ambaci sunayen su wurin aikata kisar Hanifa har sai an kammala bincike.
Kiru ya ce gwamnati ta kafa kwamiti tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan abin takaici.
Ya yi kira ga iyaye da su rikayin bincike mai zurfi kafin tura ‘ya’yan su makaranta.
Kiru ya ce daga yanzu ma’aikatar ilimi za ta rika sa ido domin duba aiyukkan makarantu masu zaman kansu a jihar.
Yadda Malami ya kashe dalibarsa
Malamin wannan makaranta Abdulmalik Tanko ya saci Haneefa ya kaita gidanshi ta yi makonni biyu tare da iyalan sa.
Da ake gabatar da su ga manema labarai, Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa gaba dayan su na tsare a hannun ‘yan sanda.
Da yake jawabi da kan sa, malamin da ya kashe Haneefa ya ce ” Bayan ya tafi da ita gidan sa, a karshe sai kawai wa bata ruwan fiya-fiya ta sha nan take ta fadi ta mutu. Daga nan yayi gunduwa-gunduwa da ita tare da wani abokin sa suka birne ta a wani gida.
Zuwa yanzu Tanko, Isyaku da Fatima suna hannun ‘yan sanda.
Discussion about this post