Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ƙorafi da gungunin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya kan cushe da zaftare ayyukan Kasafin Kuɗi na 2022, bai haɗa shi gaba, adawa, rashin jituwa ko ‘yar-tsama da su ba.
Shugaba Buhari ya yi ƙorafi dangane da yadda ‘yan majalisa su ka cusa ayyuka har 6,576 a cikin kasafin, sannan kuma su ka zaftare ayyuka har 10,733.
A jawabin da Buhari ya yi a lokacin da ya ke sa wa kasafin hannu ba da son ran sa ba, shugaban ya ce mafi yawan ayyukan da Majalisa ta cusa, duk ayyuka ne da ya kamata a ce ƙananan hukumomi da jihohi ne su ka yi su.
Cikin sanarwar da fadar Buhari ta fitar, ta ce babu wata rashin jituwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila da kuma Shugaba Buhari.
Ta ƙara da cewa kalaman na Buhari ba su haifar da rashin jituwa tsakanin sa sauran ‘yan majalisa na Tarayya ba.
Wannan jarida ta buga labarin yadda ‘Yan Majalisa 469 su ka cusa ayyukan ‘son rai’ 6576, sun zabge ayyukan Buhari 10,733.
A bisa al’adar shugabanni, lokacin da hannu a kasafin kuɗi lokaci ne na murna. To amma duk duniya ta shaida cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya cikin farin ciki a ranar 31 Ga Disamba, 2022, lokacin da ya sa wa Kasafin 2022 hannu a Fadar Shugaban Ƙasa.
Buhari dai ya sa hannu, kuma ya shaida ko kalaman sa sun tabbatar cewa ba da son ran sa ya sa hannun ba.
Bayan ya miƙa wa majalisa kasafin a cikin Oktoba, yayin da su ka maida masa, Buhari ya gano irin dubban cushe-cushen ayyuka da Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa suka yi a cikin kasafin.
Jimlar ‘yan majalisar su 469 dai sun cusa sabbin ayyuka guda 6576 a cikin kasafin, waɗanda ba su cikin waɗanda Buhari ya aika masu.
“Babban abin damuwar shi ne dukkan ayyukan da suka cusa, akasari ayyuka ne da suka kamata a ce jihohi ne da ƙananan hukumomi za su yi su, ba gwamnantin tarayya ba.” Inji Buhari a lokacin da ya ke jawabi.
A lokacin kuma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila su na wurin bikin sa wa kasafin hannu.
“Wani abin damuwa kuma, ‘yan majalisa sun zaftare yawan ayyuka 10,733 da ke cikin kasafin.
Cushe-cushen da ‘yan majalisa su ka yi, ya nuna kowane ɗaya ya cusa ayyukan ‘son rai’ har guda 14 kenan, a cikin Kasafin 2022.
A shekarun baya ‘yan majalisa sun sha cewa dokar Najeriya ta ba su ikon cusa ayyukan da su ke so a yi wa jama’a.
Bayan ya sa wa Kasafin 2022 hannu, Buhari ya fallasa canje-canjen asarƙalar da Majalisa ta yi wa kasafin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Kasafin 2022 hannu a ranar Juma’a. Sai dai kuma a cikin jawabin sa yayin da hannun, ya bayyana wa duniya irin damuwar sa kan wasu “canje-canje masu ɗaure kai” da ‘Yan Majalisa su ka banƙara ƙofar ɗakin kasafin su ka cusa a ciki.
Cikin sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari wanda ya sa wa kasafin hannu a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, ya sa hannu ne kan kasafin naira tiriliyan 17.1, saɓanin naira tiriliyan 16.3 waɗanda ya gabatar masu a cikin Oktoba.
Majalisa ta ƙara sama da biliyan 700 a cikin kasafin na 2022.
Cikin makon jiya ne Majalisar Dattawa ta ƙara masa yawa da naira biliyan 700.
Majalisar Dattawa ta yi wa Kasafin Kuɗaɗe na 2022 ƙarin naira biliyan 700.
A yanzu kasafin ya tashi daga naira tiriliyan 16.4 ya koma naira tiriliyan 17.12.
Wannan ƙarin ya zo ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Majalisar Tarayya ta miƙa kasafin.
Haka nan kuma Majalisar Dattawa ɗin dai ta maida cewa za a yi kasafin ne daidai da dalar Amurka 62, maimakon dala 57 da Buhari ya yi kasafin da farko.
Dalilin yin haka kuma shi ne saboda farashin gangar ɗanyen mai ta ƙaru bayan Buhari ya gabatar da kasafin a kan dala 57.