Sanin kowa ne cewa an samar da tsarin siyasa ne domin a inganta rayuwar alumma ta kowace fuska, hakan nema yasa aka samar da tsarin shugabanci da wakilci a bangarorin daban_daban. Tun daga matakin Jiha, Karamar hukuma da matakin kasa baki daya.
Shuwagabanni suna jagorancin Kasa ko Jihohi da kuma gunduma wato kananan hukumomi kenan a hukumance, a inda a gefe guda aka samar da tsarin wakilci domin alumma su samu saukin shigar da koken su cikin sauki wa shuwagabanni a mabanbantan majalisu. Ma’ana Kasa da Jihohi.
Babban abin takaici da ban haushi a nan gurin shi ne, wadannan yan majalisu wato wakilan alumma sun samu kasar bata kan tsarin da ya kamata hakan ne ya basu dama su ci karen su babu babbaka. A maimaikon su ringa kirkira tare da samar da dokokin da zasu ciyar da alumma gaba ko kare musu hakkokin su, sai su mayar da wannan damar ta zama hannun jari tsakanin suul da iyalan su!
Sai kaga wakilin alumma ya mayar da wasu daga cikin kwadayayyun mutane sun zama bayin sa a maimakon shi ya zama bayin su gurin kare musu hakkin su da bunkasa rayuwar su, makudan kudaden da suke hakkokin alumma ne wani mutum guda daya ya kalmashe su yana ta wadaka dasu a madadin ayyukan raya kasa da bunkasa wannan yankin da yake wakilta. Sai kaga dan majalisa ya debi kudin mutane da sunan zai bada tallafi domin canja rayuwar alumma daga wahala zuwa sauki, amma sai ya buge da kawo tsarin da zai dawwamar dasu a cikin wannan mummunan yanayin.
Yana daya daga cikin wulakanci da raina tunanin alumma da wakilan wannan zamani suke, a daidai wannan karni na ashirn da biyu da muke ciki wai a tara mutanen da suke rayuwa a cikin tsakiyar birnin Kano ace wai za a basu injin markade, firji ko babur mai kafa biyu da sunan tallafin da zai inganta rayuwar jama’a!
A daidai lokacin da ake bawa harkar ilimi da kasuwanci fifiko domin a samun ingantacciyar alumma abar alfahari a ban kasa, wai a lokacin ne wakilin alumma yake kokarin dakile tunanin alummar sa domin su cigaba da rayuwa a ma’aunin lokacin jahiliyya. Kuma ko mai wannan wakili ya dauka ya bawa alumma hakkin su ne ba wai alfarma yayi mana ba domin bai da damar taimakon alumma kafin a zabe shi ya tafi majalisar tarayya.
A nashi tunanin wakilin tsautsayin karamar hukumar fagge, burin shi alummar da yake wakilta su dawwama suna sana’r markade da achaba. Su kuma matasa a ringa tara su ana basu kudin shan kayan maye lokaci zuwa lokaci domin ayi amfani dasu gurin biyan bukatar kai!
Idan har rabawa mutane shugabancin jam’iyya da sauran daidawan mutane masu rike da mukami babura da injin markade abin afahari ne, muna addu’ar Allah ubangiji ya jarrabci yayan wakilin tsautsayi da sauran azzaluman shuwagabanni da su dawwama suna sana’ar markade ko kuma tuka mashin mai kafa biyu.