Shafin binciken gaskiyar rahotanni da labarai mai zaman kanta a Najeriya wato Dubawa, ta horas da ‘yan jarida mazauna jihar Kwara kan yadda za su rika tabbatar da gaskiyar labarai da rahotanni da ma irin kayayyakin aikin da su ke bukata dan cimma wannan buri.
SOBI FM reshen kungiyar kwadagon ‘yan jarida a Najeriya ce ta shirya horaswar wadda ita ce ta farko irinta a jihar a matsayin wani bangare na shirye-shiryen bukukuwano makon ‘yan jarida a jihar.
Burin shi ne bai wa masu aiki a kafafen yada labarai kayayyakin aiki da kwarewar da suke bukata wajen tabbatar da gaskiya ko sahihancin bayanai sakamakon irin yanayin da aka shiga na yaduwar bayanai marasa gaskiya.
A jawabin shin a bude taron, shugaban Sobi Chapel na NUJ, Dare Akogun ya ce horaswar ba taimakawa za ta yi wajen samar da bayanai ma su sahihanci kadai a jihar Kwara da Najeriya baki daya kadai za ta yi ba, za ma ta taimakawa ‘yan jarida aiwatar da alhakin da ya rataya a wuyarsu na tabbatar da cewa sun baiwa jama’a bayanan da suka kasance gaskiya kuma dai-dai.
“Muna zamani ne inda babu irin bayanan da ba’a samu a soshiyal mediya,” ya ce. “Yanzu ya zama tilas ‘yan jarida su kara illimi, da kwarewa da dabarun binciken gaskiya.”
“Wannan horaswar zai kuma taimakawa ‘yan jarida wajen tabbatar da gaskiyar bayanai a guraben aikinsu kafin su raba da sauran jama’a su karyata su kuma yi watsi da shi domin zuwan soshiyal mediya ya ta’azara muggan hanyoyin da labaran karya da yaudara ke tasiri,” ya fada
Editan Dubawa, Kemi Busari wanda ya yi takaitacciyar gabatarwa dangane da aikin jarida ga daliban ya ce wata sa’a son zuciya kan yi tasiri kan irin labaran da mutun kan zaba, da yadda suke fassarawa kafin su raba da jama’a.
Busari ya bayyana mu su irin matsalolin da ake samu dangane da bayanai, binciken gaskiya da mahimmancin tantancewa.
Silas Jonathan, daya daga cikin masu binciken Dubawa ya jagoranci sashen da ya yi magana kan irin makaman aikin da suke bukata da yadda ya dace su yi amfani da su wajen gano gaskiya ko sahihancin labarai da ma sauran bayanai.
Ya jaddada cewa duk wanda ke binciken gaskiya yana bukatar hakuri wajen gano bayanin da yak e gaskiya dangane da kalamai, ko labari/tsokaci, ko bidiyo ko kuma hoto.