Wani nazari mai zurfi da aka yi ya nuna cewa Boko Haram da Ansaru sun kasa narkewa wuri ɗaya tare da ‘yan bindigar Arewa maso Gabas.
Rahoton dai an yi shi ne a bisa doron farfajiyar ilmi, mai suna: ‘Northwestern Nigeria: A Jihadization of Banditry, or a “Banditization” of Jihad?”.
Mutum uku ne su ka haɗu su ka yi nazarin, wato James Barnet, Murtala Rufai da Abdulaziz Abdulaziz.
A bayan dai an riƙa nuna damuwa da fargabar cewa Boko Haram sun darkaki yamma, har ma sun kutsa cikin shugabannin ‘yan bindiga a yankin.
Jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Sokoto da Kebbi sun daɗe su na ɗanɗana kaifin kuɗar makaman ‘yan bindiga, waɗanda su ke kisa da garkuwa a yankin. Sanadiyyar hakan an kashe dubban jama’a kuma sun raba wasu dubban da gidajen su.
Fannin noma na ƙoƙarin ya durƙushewa a yankin, tunda manoma na tsoron zuwa gona noma, kada a sace su. An yi garkuwa da dama a cikin su, an hana su zuba girbe kayan noman su ka yi. Wasu kuma an bi su har gida an kwashe dabbobin su, an kwashe kayan abincin su, sannan kuma an banka wa rumbunan su wuta, an ƙone masu kayan abinci ƙurmus.
Tsanani ya yi tsanani a wasu yankunan karkara, domin ‘yan bindigar sun fara karɓa haraji a hannun manoman.
Hare-haren ‘yan bindiga ya haddasa hijirar dubban mutane har zuwa cikin Jamhuriyyar Nijar, yayin da aka rufe makarantun karkara saboda gudun ci gaba da kwasar ɗalibai ana garkuwa da su.
Binciken Manazartan Uku:
Yayin da James Barnet ya fitar da sakamakon a shafin sa na Twitter, ya ce sakamakon binciken su zai bai wa masu sharhi kan ‘yan ta”adda da sauran jama’a mamaki.
“Akwai dalilan da ka iya sa ‘yan ta’adda da ‘yan Boko Haram su haɗe, ganin yadda ɓangarorin biyu ke da wasu ra’ayoyi iri ɗaya da kuma dukkan su akwai wani abu da suka ƙullata a zuciyar su.
“Amma kuma hakan bai faru kusan za a iya cewa. Domin dukkan ƙoƙarin da ‘yan Boko Haram suka yi domin su haɗe da ‘yan bindiga, bai yi nasara ba kwata-kwata. Haka ma ƙoƙarin da ‘yan jihadin su ka yi domin su faɗaɗa daular su har cikin yankin Arewa maso Yamma.”
Ya ce sun ɗauki watanni su na binciken su, wanda ya haɗa da tafiye-tafiye zuwa wurare, tattaunawa da ‘yan bindiga da kuma wasu manyan ‘yan jihadin da su ka ɓalle ko su ka tuba su ka daina.
Dalilan Rashin Haɗin Kai Tsakanin Boko Haram Da ‘Yan Bindiga -James Barnet:
1. ‘Yan bindigar Arewacin Najeriya sun yi ƙarfin da ba su buƙatar su haɗe da ‘yan Boko Haram domin su ƙara ƙarfi. Sannan kuma ba su da tunani ko buƙatar zama ‘yan jihadi.
2. ‘Yan bindiga ba a ƙarƙashin shugaba ɗaya su ke ba. Gungu-gungu ne, kuma sau da yawa su na yin mummunan faɗa a tsakanin su.
Don haka Boko Haram ba za su iya shawo kan gungu-gungun ‘yan bindiga da ke zaune a yankunan dazuka daban-daban ba.
3. Yanayin hare-haren su da dalilin ɗaukar makaman su ya sha bamban da juna.
Yayin da ‘yan bindiga ba su da wata takamaimen ajanda, amma a haka sun yi ƙarfi ta hanyar kai farmaki a yankunan musulmi, su kuwa ‘yan ta’adda tafe su ke da ajandar su ta neman kafa daular musulunci, musamman ISWAP da Ansaru.
4. Su ‘yan bindiga babu ruwan su da sai an yi juyin turun sauya gwamnati ko juyin-juya-halin al’umma. Kai dai bar su ga hare-hare su na tara kuɗaɗe kawai.
Binciken na su ya nuna yadda wasu yankuna a Sokoto su ka gayyaci ‘yan Boko Haram don su kare su daga hare haren ‘yan bindiga.
Sun kuma bayyana yadda ISWAP a ƙarƙashin Al-Barnawy ta yi ƙoƙarin neman haɗe ‘yan bindiga tare da shi a cikin 2016.
Wani gudajjen ɗan Boko Haram ya shaida masu cewa Al-Barnawy ya tura manyan kwamandoji domin su karkatar da ‘yan bindiga zuwa ga ‘yan jihadi.