Hedikwatar tsaron Kasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 49 kuma ‘yan ta’adda 863 sun mika wuya a cikin makonni biyu da suka gabata.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka da yake bada bayanan aiyukkan dakarun ranar Alhamis a Abuja.
Onyeuko ya ce dakarun rundunar ‘Operation Hadin kai’ sun kashe ‘yan bindiga 37 sun kama mutum 17 daga cikinsu sannan sun kwato bindigogi 21 da harsasai 117.
Ya ce sojoji sun kwato motocin yaki hudu sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su.
Onyeuko ya ce ‘yan ta’adda da iyalen su 863 ne suka mika wuya. Cikin su akwai maza 136, mata 251 da Yara 476.
“Rundunar Sojin sama ta kai farmaki maboyar ‘yan bindiga a kauyen Arina Chili dake Tafkin Chadi a jihar Borno inda ta kashe ‘yan bindiga da dama sannan da dama sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.
Daga nan Onyeuko ya ce dakaraun rundunar ‘Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga 12 sun kuma kama wasu mutane 15.
Ya ce rundunar ta kwato makamai da suka hada da bindigogi 16, harsasai 136 da dabbobi 114.
Bayan haka Onyeuko ya ce dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven sun kama ‘yan bindiga 27 sun ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a jihohin Filato da Kaduna sannan sun kamo bindigogi biyar da harsasai 69.
A karshe ya ce dakarun rundunar ‘Operation Whirl Stroke sun kama ‘yan bindiga biyar. ya ce wadannan nasarori da aka samu na daga cikin hubbasan da dakarun Najeriya suke yi na ganin an kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.