Tashin farko inda masu bincike su ka gano an yi ragabza a kwangilar, shi ne yadda aka biya wasu ayyukan kwangiloli 10 naira biliyan 1.1 na kuɗin kwangilar, aka biya kuɗin ga wasu kamfanoni 3 duk mallakin mutum ɗaya. Sannan babu wani cikakken bayanin mai kamfanonin.
Ofishin Mai Binciken Gwamnatin Tarayya ya bankaɗo wata saɓatta-juyattar harƙallar kwangiloli har ya Naira biliyan 3 a Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, wadda aka tafka cikin 2019.
Ƙarin abin haushin ma shi ne har yanzu kwangilolin akwai waɗanda ba a yi ba, duk kuwa da an raba naira biliyan 1.1 na kwangiloli 10, waɗanda aka ba kamfanoni uku, kuma duk kamfanonin mallakar mutum ɗaya ne.
Kaɗan Daga Tabargazar Kwangilar ‘Yan Sandan Najeriya:
*Rahoto mai shafi 490 ne Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya miƙa wa Majalisar Tarayya, kuma ya bada shawarar a dawo da kuɗaɗen.
* Ya ce an yi sakaci a cikin 2019 da kuma karkatar da kuɗaɗen kwangila, biyan kwangilar da ba a yi ba, kuma ba a fara ba.
* Ya ce Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta karya dokar sharuɗɗan kwangila Sashe na 16(8) na cikin Dokar bada Kwangila ta 2007.
* Mai Bincike ya nemi Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya maida naira 1, 136, 715, 200 a Asusun Gwamnantin Tarayya, sannan ya kai rasiɗin tabbacin biyan kuɗin wurin mai bincike, domin ya tabbatar.
* Kuma kafin Sufeto Janar ya maida kuɗin, ya yi wa Majalisa bayanin yadda kuɗaɗen su ka yi shataletale suka yi ɓad-da-bami a hannun rundunar ‘yan sanda.
* An bankaɗo yadda aka biya naira miliyan 924.9 ga kwangilar da kwata-kwata ba a yi ta ba a cikin 2019.
*An biya kashi 100 bisa 100, wato naira miliyan 613.5 ga ‘yan kwangila biyu, tun ma kafin su fara komai. An biya su kuɗaɗen a ranar 17 Ga Janairu, 2019.
Discussion about this post