Watanni bayan mummunar gaba da saɓanin siyasa ya shiga tsakanin Gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Ɗanjuma Goje, har ta kai ga magoya bayan su na gwabza arangama, a ƙarshe dai manyan Gwambawan biyu sun sasanta tsakanin su.
Gwamna Inuwa Yahaya da Sanatan Gombe ta Tsakiya, Goje, sun amince a ranar Laraba cewa za su haɗa kai domin nasarar APC, ganin yadda taron gangamin jam’iyyar ya kusanto, wanda aka shirya yi a cikin Fabrairu.
An riƙa nuna hoton Yahaya da Goje a ranar Laraba, wanda aka ɗauke su tare a karon farko, tun bayan gwabza arangamar da magoya bayan su suka yi a cikin 2021.
Kafin sasantawa ranar, Yahaya da Goje sun riƙa gwada wa juna ƙwanjin ƙarfin faɗa-a-jin siyasar Gombe, lamarin da ya rikita APC a jihar.
Cikin Nuwamba ne ɓangarorin su ka gwabza, har aka kashe mutum biyar. aka ji wa da dama raunuka.
A lokacin ɓangarorin biyu sun zargi juna a rura wutar rikicin.
Amma a ƙoƙarin ganin an sasanta, a ranar Laraba ce Shugaban Riƙon APC na Kasa, Gwamna Mala Buni na Jihar Yobe, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Inuwa Yahaya da Goje sun amince su ajiye bambancin ra’ayi da ke tsakanin su, domin samun nasarar APC.
Haka Buni ya bayyana a cikin sanarwar, bayan tashi daga taro a ranar Laraba a Abuja.
Ya bayyana cewa Kwamitin Sasantawa na APC wanda ke ƙarƙashin Sanata Abdullahi Adamu da kuma tsohon Gwamnan Barno Kashim Shettima ne suka yi ƙoƙarin samun nasarar sasanta Yahaya da Goje.
Idan za a tuna, bayan gwabza arangama tsakanin magoya bayan ne, sai Gwamna Yahaya ya zargi Goje da ‘haddasa mummunan hargitsi’.
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya zargi tsohon gwamnan jihar, Ɗanjuma Goje da laifin haddasa mummunar tarzoma a jihar.
Gwamna Yahaya ya zargi Goje, wanda a yanzu sanata ne, a cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai, jim kaɗan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, a Fadar Gwamnatin Tarayya, Abuja a ranar Talata.
Wannan furuci na Gwamna Yahaya ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wata mummunar arangama da aka yi tsakanin magoya bayan gwamnan da na Sanata Goje.
Ƙazamin faɗan dai ya haddasa rasa rayukan mutum biyar.
Yayin da Goje ya zargi Gwamna Yahaya cewa shi ya shirya kai wa tawagar sa hari, inda magoya bayan gwamnan su ka hana Goje shiga Gombe, ita kuwa jam’iyyar APC reshen jihar Gombe, ta yi wa Goje barazanar cewa ya bai wa Gwamna haƙuri, ko kuma ta dakatar da shi daga jam’iyyar APC a jihar.
Da ya ke wa manema labarai jawabi, Inuwa Yahaya ya ce yanzu komai ya dawo daidai a jihar, tun bayan arangamar da aka yi.
Ya ce jama’ar Gombe sun bijire wa Goje ne, wanda a baya aminin sa ne na ƙut-da-ƙut da kuma na siyasa.
“Sanata Ɗanjuman dai da ku ka sani, shi ne ya haddasa rikicin, har ta kai ga an rasa rakuya kuma an lalata dukiyoyin jama’a.
“Mu dama abin da mu ke gudu kenan. Kowa ya san Goje ne ya kafa ‘yan kalare a Gombe, waɗanda suka riƙa kashe mutane.
“To ni ba zan amince da ‘yan kalare a Gombe ba. Kuma duk mai hannu a Kalare tilas ba za mu bari ya biya buƙatar sa da su ba. Da yardar Allah sai mun kawo ƙarshen kalare a Gombe.
An tambaye shi batun ƙorafin da Goje ya shigar Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, inda ya ce wasu jami’an gwamnatin Gombe sun yi barazanar kashe shi, sai Gwamna Yahaya ya ce ai bincike zai tabbatar da gaskiyar zargin sa ko akasin haka.
An tambaye shi batun kokawar sake cin zaɓen sa a 2023, sai ya ce “Allah ne kaɗai ya san wanda zai kai shekarar 2023 ɗin, tsakanin sa da Goje.”