Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa akwai matuƙar buƙatar yi wa dokar mafi ƙarancin ilmin da ake buƙata ga wanda zai shugabanci Najeriya zai mallaka kafin tsayawa takara.
Ba a kan shugaban ƙasa kaɗai Gbajabiamila ya tsaya ba, ya kuma ƙara yin kira a ƙara gejin matsayin ilmin waɗansu muƙaman.
Kakakin ya yi wannan magana a lokacin da ya ke jawabi wuri Bukin Yaye Ɗalibai Karo na 52 a Jami’ar Legas (UNILAG), da ke Akoka.
Ya ce Sashe na 131 (d) na Dokar 1999 wanda ya ce mai iyar zurfin ilmin sakandare zai iya shugabancin Najeriya, bai yi wa yanayi da damanin yanzu daidai ba. Musamman ya ce yanzu ci gaba ya yi nisa sosai, ba kamar da can baya ba.
“Na haƙƙaƙe kuma na yi amanna cewa Majalisar Tarayya ya kamata ta sake duba Sashe na 131 (d) na dokokin 1999, domin a ƙara zurfin ilmin wanda zai shugabanci Najeriya zai mallaka. Haka su ma ‘yan Majalisar Tarayya da na Dokoki, duk kamata ya yi a ce sun wuce buƙatar mallakar kwalin shaidar kammala sakandare kaɗai.”
“Yayin da muka rage yawan shekarun ɗan takara, to kuma ya kamata mu ƙara darajar imanin su, domin ta hakan zai ba mu damar samar da shugabanci mai nagarta.” Inji Gbajabiamila.
Kakakin ya ce yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen 2023, ai a 2019 Najeriya, Majalisa ta yi nasarar gyaran shekarun ‘yan takara, inda ta rage yawan shekarun masu takarar manyan muƙamai, domin a samu matasa su shiga takara, a lokacin da aka bijiro da ‘Not Too Young To Run.”
Gbajabiamila, wanda shi ma a ya yi karatu a UNILAG ɗin, wato tsohon ɗalibin ta ne, ya yi magana kan matsalar ilmi a Najeriya, inda ya ce irin yadda ake tafiya a yanzu, ana jiran sai gwamnatin tarayya ta bada tallafi sannan harkar ilmi za ta motsa, ba abu ba ne mai fitar da ƙasar nan daga ƙalubalen fannin ilmi.
Ya ce Majalisa na nan ta na ƙoƙarin fito da tsarin bunƙasa ilmin manyan makarantun jami’o’i da manyan kwalejojin fasaha da na ilmi, domin a riƙa bai wa ɗalibai lamunin kuɗaɗe ba tare da ruwa ba. Kuma ana nazarin yadda za su riƙa biyan kuɗaɗen.