Duk da irin munin da korona ta yi da illar da ta yi wa tattalin arzikin duniya, hakan bai sa ta yi wa hamshaƙan attajiran Afrika su 18 wani lahani ga arzikin su ba a cikin 2021.
Binciken Forbes ta fito da cewa arzikin hamshaƙan attajiran Afrika su 18, bisa jagorancin babban dakaren su Aliko Ɗangote, ya ƙaru da kashi 15 bisa 100 a cikin 2021.
Watau kenan su 18 ɗin ƙarfin arzikin su ya kai dala biliyan 84.9 kenan.
Wannan ya nuna irin maƙudan kuɗaɗen da su Ɗangote su ka ƙara samu kenan, sai kuma irin yadda su ke ci gaba da samun nasibin kasuwa.
Cikin 2014 ƙididdigar Forbes ta nuna attajiran Afrika 28 sun mallaki dala biliyan 96.5. Sai dai kuma a yanzu za a iya ganin cewa mutum 18 ne kaɗai daga cikin su suka mallaki har dala biliyan 84.9.
Ƙididdigar ƙwaƙwaf ɗin dai mujallar Forbes ce ta fito da shi ne a ranar Litinin.
Amma kuma ta tsame sunayen biloniya Mo Ibrahim, wanda ɗan asalin haifaffen Sudan ne, amma kuma a yanzu ɗan ƙasar Birtaniya ne.
Kuma ta tsame dukiyar biloniya Mohammed Al-Fayed, mutumin Masar, amma kuma a Landan ya ke yin duk harkokin sa, ba kamar irin su Ɗangote ba da harkokin su a cikin Afrika.
Amma kuma Strive Masiyiwa, attajirin nan ɗan Zimbabwe ya na cikin jerin sunayen su Ɗangote 180, duk da a Landan ya ke zaune, saboda kamfanin sadarwar sa na Telecom a Afrika ya ke hada-hadar sa.
Ko Dubu Ta Taru: Yadda Arzikin Ɗangote Ya Yi Daidai Da Arzikin Ƙasar Senegal:
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa “samun ƙarin dala biliyan 1.3 cikin mako biyu ya sa arzikin Ɗangote ya yi daidai da arzikin Sanagal gaba-ɗaya.”
Ƙarfin arzikin Aliko Ɗangote ya yi tashin gwauron zabi, inda a farkon watan Janairun 2022 ɗin nan ya ƙaru da dala biliyan 1.3 a cikin makonni biyu.
Wannan kuwa babban nasibin kasuwa ne ga shi kan sa da kuma masu hannayen jari a kamfanin simintin Dangote Cement Plc.
Ƙididdigar da Bloomberg su ka yi cikin wannan makon ta nuna cewa a yanzu ƙarfin arzikin Ɗangote ya kai dala biliyan 20.4, watau kwatankwacin ƙarfin tattalin arzikin ƙasar Sanagal baki ɗayan ta, ƙwai da kwarkwata.
Bankin Duniya ne ya ƙiyasta tattalin arzikin Sanagal cewa baki-ɗaya bai wuce dala biliyan 20.9 ba.
A lissafin yawan al’ummar ƙasar Sanagal da Worldmeter ta yi a ranar 20 Ga Janairu, 2022 ta ce yawan jama’ar Sanagal ya kai mutum miliyan 17,246,442.
Dangote ya ƙara samun waɗannan maƙudan kuɗaɗe a cikin makonni biyu ne ta hanyar tsakurar kaɗan daga hannayen jarin kamfanin ya sayar.
Ƙarfin Darajar Kamfanin Dangote Cement A Kasuwa:
Wannan ƙarin kashi 11 bisa 100 na hannayen jari da kamfanin ya samu, sun kai Dangote Cement a yanzu darajar sa a kasuwa ta kai naira tiriliyan 4.9.
Lissafin waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba ya yiwuwa da takardun kuɗi. Sai dai mai lissafi ya shafa wa kan sa lafiya, ya kira su fan-tokare-sama ko fan-cika-teku.
Banda sauran masana’antu da kamfanonin sa, a yanzu haka Dangote ya na gina matatar ɗanyen mai a Legas, wadda idan an kammala ta cikin wannan shekara ta 2022, za ta riƙa tace ganga 650,000 a kowace rana.
Dangote Refinery za ta zama matatar mai mafi girma ta ɗan kasuwa mai zaman kan sa a duniya. Matatar ta nunka faɗin unguwar Tsibirin Victoria Island na Legas kusan sau shida.
Cikin wata hira da David Pilling na jaridar Financial Times ta Landan ya yi da Dangote a 2018, ya ce ya ƙudiri aniyar sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal FC da ke Landan.
Amma ya ce sai bayan ya kammala ginin Matatar Ɗanyen Mai ta Legas tukunna.
“Haka atttajirin ya faɗa, kan sa tsaye, kamar wanda zai sayi wata kaza ko zakara a kasuwa Ko wayar GSM ta zamani da ‘yan zamani ke yayi, wato IPhone.” Inji Pilling.
Wani abin birgewa ga Dangote, shi ne bai mallaki gidaje a kowace ƙasa ba, sai a Najeriya. Haka ya faɗa a wata tattaunawa da aka yi da shi, shekaru uku ko biyu da suka gabata.