Zargi: Wani sanannen shafin da ke tsokaci kan kwallon kafa, wanda aka fi sani da football world a turance ya yi zargin cewa kungiyar kwallon kafar Saliyo ta tafi Kamaru a jirgin ruwa don ba ta da halin sayen tikitin zuwa gasar ta AFCON da jirgin sama.
Shafin Football World, da ke tsokaci kan kwallon kafa, wanda kuma ya ke da mabiya fiye da milliyan, ya wallafa wadansu hotunan ‘yan wasan Saliyo bayan karawarsu da kungiyar kwallon kafar Aljeriya – the desert foxes, inda suka tashi ba ci.
Da ya ke bayani kan hazaka da juriyar kungiyar kwallon kafar ta Leone Stars, Football World ya yi zargin cewa a jirgin ruwa kungiyar ta tafi gasar ta Kamaru. A cewar rahoton kungiyar kwallon kafar kasar ta SLFA ba ta da kudi. Dan haka ‘yan wasan sai da suka yi tafiyar kilometa 2000 a jirgin ruwa daga Freetown zuwa Kamaru.
“ma’abotan su sun yi bankwana da su kafin tawagar ta isa Kamaru a jirgin ruwa sakamakon karancin kudin sayen tikitin jirgin sama. Dan haka sun yi tafiyar da ta wuce kilometa 2000…..” a cewar wani bangaren labarin da suka wallafa.
Rahoton na Football World ya biyo bayan wasa mai kayatarwar da Leone Stars ta yi a rukunin Group E bayan da suka kara da zakarun gasar na bara wato Aijeriya inda aka kammala wasan ba ci ko daya. Wannan ne karon farko da Leone Stars ke halartar gasar AFCON a shekaru 26.
Ganin cewa mutane kusan dubu 90 sun yi ma’amala da labarin a shafin Facebook a yayin da wasu 8,000 kuma su ka yi tsokaci kan labarin har ma da wadanda suka yarda da wannan zargin, Dubawa ta kuduri aniyar tantance gaskiyar labarin dan kawar da wannan zargi.
Tantancewa
Football World ba ta fayyace cewa akwai rafi a tsakanin tashar jirgin saman Saliyo mai suna Lungi International da tashar jirgin ruwan zuwa yankin kudancin tashar da ke Freetown. Wannan na nufin idan har mutun zai je tashar jirgin saman a kan lokaci dole sai ya shiga jirgin ruwa. Idan ba haka ba sai ya yi tafiya mai nisa da mota daga Freetown zuwa Lungi ko kuma ta garin Port Loko wanda shi ma ya ke da tazarar gaske.
Babu shakka akwai bidiyon da ya nuna ma’abota kungiyar kwallon kafan suna yabawa ‚yan wasan yayin da suke shiga jirgin ruwa, amma jirgin ruwan ya kai su tashar jirgin saman Lungi ne. Bidiyon ya nuna ‚yan wasan suna tabbatarwa ma’abotansu cewa za su taka rawar gani a gasar. Daga bidiyon mutun zai gani wai jirgin ruwan na haya ne ko kuma tasin da zai kai su jirgin saman, ba wai Kamaru ba kamar yadda labarin Football World ke zargi.
Bacin haka, daya daga cikin ‘yan wasan Kei Kamara, ya yi bidiyo na kai tsaye a shafin Instagram inda ya nuna jirgin ruwan na sauke su kafin suka sake shiga wata mota kirar bus wadda ta karasa da su zuwa tashar jirgin saman har ma ya bayyana hakan, “dole sai mun shiga bus kafin mu kai jirgin saman da zai kwashe mu.” Ya bayyana jim kadan bayan da suka sauka daga jirgin ruwan.
Akwai ma hotunan tawagar ta Saliyo wadanda aka dauka sadda suke tashar jirgin sama, wadanda su ma sun karyata zargin na Football World. Kamar yadda aka gani a shafin tiwitan kungiyar kwallon kafar kasar, Jirgin saman yankin Scandanavia mai suna Scandanavian Airlines ne aka yi shatta dan kai kungiyar kwallon kafar ta Leone Stars Kamaru.
Dubawa ta kuma tuntubi Ibrahim Kamara, shugaban yada labarai na Kungiyar Kwallon Kafar Saliyo wanda shi ma ya halarci gasar ta AFCON a Kamaru. Kamara ya karyata wannan zargin inda ya ce shatan jirgi aka yi dan kawo ‘yan wasan.
A Karshe
Duk da cewa ‘yan wasan sun shiga jirgin ruwa da za su baro Freetown, ba gaskiya bane yadawa dake yi wa sun tafi kasar Kamaru a jirgin ruwa wai dan ba su da kudin sayen tikitin jirgin saman da zai kai su gasar kwallon kafar na AFCON. Dole sai an shiga jirgin ruwa kafin a kai tashar jirgin saman kasar. Kuma an yi shatan jirgi ne ya kai su.