Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya yi iƙirarin cewa ayyukan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi na raya ƙasa, sun zarce ayyukan da gwamnatin PDP ta yi yawa a cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki.
Ya yi wa mulkin PDP kuɗin-goro, inda ya ce gaba ɗaya mulkin shugabannin PDP ɗin uku da aka yi ya ke nufin cewa ayyukan su a jimlace ba su kai ayyukan Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Fashola ya yi wannan iƙirarin ne a yayin da ya ke jawabi wurin wani taron tattauna batun dangantakar gwamnati da al’umma a aikace.
Wasu gidajen radiyo a Kano dai sun riƙa watsa shirin kai-tsaye, inda wasu jama’a su ka samu damar ganawa da ministan a kan batun mulkin da su ke kai.
A wurin taron dai Fashola ya riƙa nuna wasu hotunan ayyukan da Gwamnatin Buhari ta yi, kuma ya na nuna irin yadda jama’a ke yabawa da ayyukan. Duk ya yi haka ne domin ya nuna irin gagarimin aikin inganta rayuwar al’umma da wannan gwamnatin ta aiwatar a cikin shekaru shida kaɗai, duk kuwa da cewa kuɗaɗen da Gwamnatin APC ta samu ko kaɗan ba su kamo ƙafar kuɗaɗen da Gwamnatin PDP ta samu a cikin shekaru 16 ɗin mulkin ta ba.
“Yi wa al’umma ayyukan raya ƙasa ita ce halastacciyar hanyar da za a raba kuɗi a cikin tattalin arziki daga hannun gwamnati can daga sama zuwa ƙasa.”
Minista Fashola dai shi ne Ministan Ayyuka tun daga hawan APC mulki cikin 2015 har zuwa yau.
“Tsawon shekaru shida kenan da suka gabata tuni wannan gwamnatin ta na yin abin da gwamnatin Amurka ke ƙoƙarin ta ga ta yi. Wato batun amincewa da kudirin dokar gina ayyukan raya ƙasa. Kuma har yanzu ana sa-toka-sa-katsi kan wannan kudirin a Majalisar Amurka.”
Fashola ya kuma ƙi yarda da masu cewa wai da APC da PDP duk ɗaya ne a yanzu. Ya ce ba ɗaya ba ne, duk da dai wasu ‘yan PDP ɗin sun fice sun koma cikin su Fashola a APC.
“Damar da PDP ta samu har ta tsawon shekaru 16 domin ta yi wa ‘yan Najeriya aiki, amma ba ta yi ba. Sai ga shi mu APC mun yi ayyukan da PDP ta kasa yi cikin damar da muka samu ta shekaru shida kaɗai.
“To ko ta fannin inganta rayuwar al’umma ɗin nan da muke yi a faɗin ƙasar nan, ai mun bambanta da PDP. Ballantana ma ba bambanta kaɗai muka yi ba, mun zarce su fintinkau.” Inji Fashola.
Yayin da ya riƙa lissafa ayyukan titina da gadoji a faɗin ƙasar nan, Fashola ya ƙara da cewa “yanzu haka ana ci gaba da gina gidaje a jihohi 34 da Abuja. Sannan kuma ana gina Sakateriyar Gwamnatin Tarayya a jihohin Anambra, Nasarawa, Bayelsa, Zamfara, Osun da Ekiti.”