Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa mutum 387 sun rasa rayukansu a dalilin rikicin kabilanci a kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru daga shekarar 2020 zuwa 2021.
El-Rufa’i ya fadi haka ne a taron da ya yi da sarakunan gargajiya da manyan hafsoshin tsaro na jihar da aka yi a fadar Agwatyap, A̠tak Njei a Zangon Kataf.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya wakilce gwamna El-Rufai a wurin taron.
Aruwan ya kara da cewa mutanen da suka rasa rayukan su duk a sanadiyyar rikicen kabilanci ne tsakanin kabilun Atyap, Fulani, Chawai, Irigwe da Hausawan dake zama a kananan hukumomin.
Gwamnatin Kaduna ta kira wannan taro ne domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya a waɗannan kananan hukumomi.
“A shekarar 2020 mutane 114 ne suka rasa rayukansu a Zangon Kataf mutum 28 a Kauru. A shekaran 2021 mutum 186 sun mutu a Zangon Kataf mutum 59 a Kauru. A jimlar mutum 387 sun mutu a shekara biyu.
“A shekaran 2021 mutum 100 sun ji raunin harsashi a jikinsu a kananan hukumomin.
“An kona gidaje da gonaki sannan an kashe dabobbi tattalin arzikin yankin ya rushe.
“A dalilin haka ya kamata duk mu hada hannu domin ganin an samar da zaman lafiya a yankin.
Bayan haka Dan majalisar dokoki na jihar dake wakiltan yankin Zangon Kataf da Jaba Amos Magaji ya goyi bayan samar da zaman lafiya a yankin.
Agwatyap Dominic Yahaya da sarkin Chawai Yahaya Mohammed sun dauki alkawarin hada hannu da gwamnati domin Samar da zaman lafiya a yankin su.
Shugaban karamar hukumar Zangon Kataf Francis Sani da shugaban karamar hukumar Kauru Bashir Dawaki sun yaba wa gwamnan jihar na shirya wannan taro domin samar da zaman lafiya a yankin.
Shugaban rundunar Operation Safe Haven dake aiki a yankin Tony Opurum da kwamandan ‘yan sandan Kafanchan Danladi Ibrahim sun bayyana cewa jami’an tsaro za su ci gaba da kokarin ganin lallai an kawo karshen kashe-kashen juna a tsakanin mazauna yankunan da ba su ga maciji.
Matakan da aka ɗauka
Abu biyu da aka zartas a taron sune mutane su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin su sannan kuma shugabanni sun yi kira da a koma kan teburin sulhu a tattauna rikicin filiye da yaki ci yaki cinyewa da ya samo asali tun a 1992.
Discussion about this post