Jima’i na daya daga cikin abubuwan dake sanya mutum cikin nishadi a rayuwa wanda idan babu shi mutane da dama za su shiga cikin kunci da damuwa na rayuwa.
Baya ga haihuwa jima’i na kara dankon soyayya tsakanin masoya, samar wa wasu kariya daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, kawar da damuwa da saka nishadi.
Sai dai kuma duk abinda da ke da amfani yana kuma da matsaloli musamman idan ana yawan yin babu kakkautawa.
Yawan yin jima’i na iya cutarwa musamman ga mace.
Hakan na yawan faruwa saboda karfin namiji da mace ba daya bane sannan sha’awar namiji da na mace ma ba daya bane.
A dalilin haka ya kamata a rika kula saboda kada wani ya cuci wani garin neman gamsuwa.
Hanyoyi bakwai da yawan jima’i ke cutar da mace.
1. Kumburar da gaban mace
Kumburin na aukuwa ne idan mace na yawan yin jima’i babu kakkautawa.
Baya ga kumburin wasu bangarorin gaban mace ma na iya samun matsala da hakan ke sa gaba ya rika yi wa mace zafi ko ka ga mace tana tafiya a banbankare.
2. Kamuwa da cutar sanyi
Matan da ke yawan yin jima’i na yawan kamuwa da cutar sanyi.
Kamata ya yi mace ta rika amfani da korona roba domin kare kanta ko kuma idan mijinta ne ta nemi magani domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka.
3. Yin fitsari da zafi
Yawan jima’i na sa mace ta samu matsalar yin fitsari da zafi saboda rashin hutawa.
Mace za ta iya gasa gaban ta da ruwan zafi tare da shafa man kade domin samun sauki.
Sannan bada rata kafin a yi jima’i ba a rika yi akai-akai ba na cikin hanyoyin guje wa samun irin wannan matsala.
4. Ciwon baya
Ciwon baya a jima’i alama ce dake nuna wa mutum cewa naman dake bayan mutum sun kwaye saboda ana yawan takura baya.
Ciwon baya alama be dake nuna wa mace da ta rika bada rata a yin jima’i.
5. Yawan gajiya
Jima’i na yawan gajiyar da mutum don hakan ya kamata a rika hutawa musamman idan ana cikin yin jima’in ne.
6. Yawan Jin kishi
Saboda zufa da ruwan da ake fitarwa a lokacin yin jima’i ya sa mutum kan ji kishi a lokacin da ake jima’i.
Yawan yin jima’i na sa jikin mutum ya bushes musamman gaban mace.
Yawan shan ruwa, cin ‘ya’yan itatuwa musamman kankana da bada rata a ranakun da ake saduwa na taimakawa wajen guje wa irin wannan matsala.
7. Karya garkuwar jiki
Jikin mutum na fitar da sinadarin ‘Prostaglandin E-2’.
Wannan sinadarin na fita be idan ana yawan takura jiki ko Kuma idan wasu namomin jiki sun kwaye wanda hakan kan sa mutum yin zazzabi da ciwon jiki kafin jikin mutum ya warke.
Yawan fitar da wannan sinadari na iya karya garkuwar jikin mutum.