Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun ceto mutum 97 dake tsare a hannun ‘yan bindiga a dazukan dake yankin ƙaramar hukumar Tsafe da Shinkafi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba El-kana ya sanar da haka a taron manema labarai ranar Talata a garin Gusau.
El-kana ya ce rundunar ta yi nasarar ceto wadannan mutane ne a dalilin aiyukkan da jami’an tsaro suka rika yi a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji da kuma mabuyar shahararren ɗan bindiga Bello Turji.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa a ranar 3 ga Janairu rundunar ƴan sandan dake aiki a yankin Shinkafi sun samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane sun gudu sun bar mutanen da suka yi garkuwa da su a daji.
Tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga da wasu tubabbun ‘yan bindiga rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar ceto mutum 68.
Sakamakon bincike ya nuna cewa mutanen sun yi sama da watanni uku a hannun maharan.
Daga cikin wadanda jami’an tsaron suka ceto akwai maza manya 33, yara maza 7, yara mata 3, da mata 25 inda a ciki akwai masu ciki da masu shayarwa.
‘Yan bindigan sun sato wadannan mutane daga kauyukan dake kananan hukumomin Magarya, Maradun da Gusau a jihar Zamfara sannan da kauyukan dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Bayan haka El-kana ya ce a wannan rana kuma ‘yan sandan dake aiki a yankin Tsafe sun ceto mutum 29 dake tsare a dajin Kalgo a karamar hukumar Tsafe.
Bincike ya nuna cewa mutanen sun yi sama da kwanaki 60 a hannun ‘yan bindiga sannan sun sato su daga kauyuka 3.
Kauyukan sun hada da Adarawa, Gana da Bayawuri dake karamar hukumar Gusau.
Daga cikin wadanda aka ceto akwai yara maza 5 da mata 25 inda a ciki akwai masu ciki da masu shayarwa.
Ya ce rundunar ta gano cewa shahararren mai garkuwa da mutane Ado Aleru ne ya yi garkuwa da wadannan mutane.
El-kana ya ce an kai mutanen asibiti domin likitoci su duba su sannan daga nan za su damka su hannun gwamnatin jihar Zamfara kafin a maida da su garurruwan su.