Ƴan bindiga sun kashe wasu mutane harda ƴan sanda da sojoji a ciki a karamar hukumar Danko Wasagu, jihar Kebbi.
Kakakin ƴan sandan jihar ya bayyana cewa maharan sun kashe sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya sannan da wasu mutane 13 a ƙauyen ɗankade dake karamar hukumar Danko Wasagu.
Bayan haka ya ƙaryata rahotannin da ake ta yaɗawa cewa wai mutum sama da 50 ne mahara suka kashe.
” Maharan da suka aikata wannan abu sun shigo ne daga Zamfara. Amma kuma suma ba su ji da daɗi ba domin dakarun mu sun ragargaje su. An kashe ƴan bindiga da dama duk da dai sun kashe sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya.
Jihar Kebbi ita ma tana fama da hare-haren ƴan bindiga matuka, domin a cikin shekarar da ta gabata ƴan bindiga suka sace daliban makaranta.