Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ce akwai tuhume-tuhume guda 9 da ɗan Gwamnan Bauchi Bala Minista zai fuskanta a kotu, waɗanda su ka shafi harƙalla da wuru-wurun kuɗaɗe, waɗanda yaron ya aikata, a lokacin da mahaifin yaron ke Ministan Abuja.
A ranar Talata ce Babban Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya ce tuhume-tuhumen sun haɗa da laifin ƙin bayyana wa EFCC adadin kuɗaɗen da ke cikin asusun sa da ke bankuna daban-daban, zamba, da fojare.
Mai Shari’a ya ce ƙwararan hujjojin da ke gaban kotu sun sa tilas a ci gaba da tuhumar wanda ake zargin da laifuka 9 daga cikin guda 20 da a farko EFCC ta gurfanar da shi a kan su.
Mai Shari’a ya yi watsi da sauran canje-canje 11, waɗanda ke da nasaba da karkatar da kuɗaɗe, saboda EFCC ta kasa gabatar da ƙwararan hujjoji.
Haka nan kuma kotu ta sallami sauran mutun huɗu da ake tuhumar su tare da ɗan Bala. Mai Shari’a ya ce hujjojin da EFCC ta gabatar ba su kama mutanen da laifin karkatar da kuɗaɗe ba, a cikin tuhume-tuhume 11 da aka yi masu.
Ɗan Bala dai ya shiga jula-jular zargin sa da sayen kadarori na naira biliyan 1.2 a cikin Abuja, tsakanin 2014 zuwa 2015.
EFCC ta ce ya sayi gidajen a lokacin da mahaifin sa ke Ministan Abuja.
Shi ma Bala Mohammed ya na fuskantar tuhume-tuhume a kotu. An tsaida ta sa ne saboda ya samu kariya bayan an zaɓe shi Gwamnan Bauchi, a watan Mayu, 2019.
Za a ci gaba da shari’ar sa bayan ya kammala wa’adin sa na gwamna a Bauchi.