Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Misikilu Mojeed, Babban Editan PREMIUM TIMES murnar lashe zaɓen zama Shugaban Cibiyar Kare Haƙƙin ‘Yan Jaridu ta Duniya (IPI), Reshen Najeriya.
Haka nan kuma ya tara Ahmed Shekarau na Daily Trust murnar zama Sakatare a zaɓen wanda aka yi a ranar Alhamis.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Buhari, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya bayyana Mojeed a matsayin gwarzo kuma jajirtaccen ɗan jarida, wanda harziƙancin sa zai ƙara wa cibiyar karsashi da ƙara jajircewar wajen kare haƙƙin ‘yan jarida, irin turbar da wannan gwamnati ta sa a gaba.
Ya kuma taya shugabannin da su ka sauka murnar kammala wa’adin su lafiya.
Premium Times ta buga yadda aka zaɓi Babban Editan Kamfanin PREMIUM TIMES ya zama Shugaban Cibiyar Kare Haƙƙin ‘Yan Jarida ta Duniya, Reshen Najeriya.
Babban Editan PREMIUM TIMES Musikilu Mojeed ne aka zaɓa sabon Shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin ‘Yan Jarida ta Duniya, Reshen Najeriya (IPI).
Mojeed ya samu lashe zaɓen ba tare da karawa da kowa ba, inda ba shi da abokin takara, kuma kowa ya amince da shi.
An yi zaɓen ne a Abuja a ranar Alhamis, kamar yadda sanarwar da IPI ta fitar a ranar Juma’a, bayan kammala taron Majalisar Ƙolin IPI ɗin, wanda a wurin ne aka zaɓi sabbin shugabanni.
An zaɓi tsohon editan Peoples Daily kuma Babban Manajan Harkokin Kasuwancin Daily Trust a yanzu, wato Ahmed Shekarau a matsayin Sakatare.
Shekarau ya lashe yawancin ƙuri’un da aka jefa, inda ya doke aboki takardar sa Qasim Akinreti, wanda Mataimakin Darakta ne a Tsarin Kafar Sadarwar Zamani a Muryar Najeriya (VON), Abuja.
Sanarwar da ɗaya daga cikin Manyan Shugabannin Gudanarwa na IPI, Raheem Adedoyin ya sanar da zaɓen Rafatu Salami a matsayin Ma’ajin Kuɗaɗen Cibiya.
An zaɓi Rafatu kai tsaye ba tare da ta samu mai yin takara da ita ba. Rafatu Matainakiyar Darakta ce a VON.
Mutum uku ne Kwamitin Zaɓen Cibiya su ka gudanar da zaɓen, waɗanda su ka haɗa da Kabiru Yusuf Shugaban Jaridar Daily Trust, Kadaria Ahmed da kuma Adedoyin a matsayin mamba. Kuma tuni lauya Zainab Musa ta rantsar da su.
IPI ƙungiyar manyan editoci da mawallafan jaridu ce ta duniya, wadda aikin ta ya fi ƙarfi wajen tabbatar da kare haƙƙin ‘yan jarida da gidajen jaridu a duniya da kuma ƙwatar masu ‘yanci.
Mojeed gogaggen ɗan jarida ne da ya shahara a duniya wajen iya zaƙulo labarai da fallasa badaƙalar da shugabbani ke binnewa a ƙarƙashin ƙasa. Kuma ya sha samun lambobin yabo a wannan fannin.
A Najeriya, jaridar sa PREMIUM TIMES ta shahara wajen buga labaran ba-sani-ba-sabo.
Discussion about this post