Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta soke takarar Andy Uba na APC a zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar cikin watan Nuwamba.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin, a lokacin da ya bayyana cewa Andy Uba ba halastaccen ɗan takara ba ne, domin an tsayar da shi takarar gwamnan Anambra ƙarƙashin APC, a haramtaccen zaɓen fidda gwani na APC ɗin.
Ekwo ya ce wanda ya shigar da ƙara, wato George Moghalu ya gamsar da kotu cewa APC ba ta shirya sahihin zaɓen fidda gwani ba, wanda har Uba zai cancanci tsayawa a matsayin takarar zaɓen gwamna, wanda aka yi a ranar 6 Ga Nuwamba, 2021.
Kotu Ta Saɓule Wa Andy Uba Ɗan Kamfai A Kasuwa:
Mai Shari’a ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta goge sunan Andy Uba a jerin sunayen ‘yan takarar zaɓen gwamnan Anambra a 2021.
Wannan hukunci na nufin ko da Andy ya lashe zaɓen, to kotu za ta iya ƙwacewa ta bai wa jam’iyyar da ta yi na biyu, ko kuma ta bai wa Moghalu.
Bugu da ƙari, kotu ta umarci APC ta biya George Moghalu naira miliyan 22.5, waɗanda ramuwa ce za a yi masa ta kuɗin fam ɗin takara a ƙarƙashin APC da ya yanka.
A zaɓen dai wanda aka yi ranar 6 Ga Nuwamba, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Charles Soludo ne ya lashe zaɓen, shi kuma Andy Uba ya zo na uku.