Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama matar tsohon shugaban hukumar kwastam Rahila Yakubu da laifin yi wa ‘yar kishiya duka da tabarya saboda ba ta yi aikin da ta saka ta ba.
Rahila ta yi wa ‘yar kishiyarta Hafsat Argungu targade a hannu sannan ta ji mata rauni a kai, kafafuwa da sauran bangarorin jikinta.
Ta ce Hafsat kazamiyar yarinya ce sannan tana yi mata dauke-dauke.
Rahila ta fara kula da Hafsat tun tana da shekara daya a dalilin mutuwar auren mahaifiyar ta da mahaifinta.
‘Yan sanda sun kama Rahila bayan hotunan raunin da Hafsat ta ji ya kareda shafukan sada zumunta a yanar gizo.
Dukan da matar mahaifina ke mun
Hafsat ta ce tun da take hannun Rahila take shan dukan tsiya.
Ta ce Rahila da danta kan taru su yi mata dukan tsiya akan laifin da bai taka kara ya karya ba sannan idan dukan bai isa ba sai su watsa mata ruwan sanyi a jiki ko su aske mata kai.
Hafsat ta ce a ranar da Rahila ta yi mata duka ta tabarya ta sata yin wanke-wanke ne, ban samu na iya yi ba da wuri sai ta hauni da duka.
“Daga nan sai ta saka ni wankin kaya amma sai na gudu saboda dukan farko da ta yi mun.
“Da na dawo sai ta dauki tabarya ta rika rankwala min ta ko-ina.
Kodinatan hukumar kare hakkin dan Adam ta ƙasa dake jihar Sokoto Hali Tambari ya yi tir da hukuncin da Rahila ta yi wa Hafsat.
Tambari ya ce za a hukunta masu cin zarafin yara kanana domin zama darasi ga masu aikata irin haka nan gaba.
Daga nan uwar gidan gwamnan jihar Mariya Tambuwal ta ce za ta hada hannu da hukumar kare hakkin dan Adam ta ƙasa domin ganin an hukunta masu cin zarafin yara a jihar.
Discussion about this post