Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina, ya ce ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kashe mutane, sun fi dabbobi dabbanci.
Masari ya bayyana haka a Sokoto, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnonin Arewa maso Yamma, inda su ka je ta’aziyyar mutane 23 matafiya da ‘yan bindiga su ka banka wa wuta a cikin mota, su ka ƙone ƙurmus.
Masari ya ce jami’an tsaro su kaɗai ba za su iya kawar da ‘yan bindiga ba.
A kan haka ne ya ce lokaci ya yi da jama’a za su tashi su kare kan su. Ya ce ta haka ne kawai za a iya taimakon jami’an tsaro a murƙushe ‘yan bindiga.
A na sa jawabin, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya ce kafa wa ‘yan bindiga dokar-ta-ɓaci ne kaɗai zai iya sa sojoji su gama da su baki ɗaya.
Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, kafa dokar-ta-ɓaci a kan ‘yan bindiga ne kaɗai zai iya bai wa sojoji damar kutsawa cikin dazuka, su yi kan-mai-uwa-da-wabi, domin su kakkaɓe ‘yan bindiga.
Tambuwal ya yi wannan shawara ce ranar Laraba a Sokoto, lokacin da ya ke karɓar tawagar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma.
Tawagar wadda ke ƙarƙashin Gwamna Aminu i na Katsina, sun je Sokoto ne domin yin ta’aziyyar matafiya 23 da ‘yan bindiga su ka banka wa wuta, su ka ƙone ƙurmus.
Tambuwal ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa dokar-ta-ɓaci, domin ta haka ne “za a bai wa jami’an tsaro ƙarfin umarnin bisa doka, yadda za su yi amfanin da dukkan ƙarfin sojoji su murƙushe ‘yan bindiga.”
Tambuwal ya ce yin wannan dokar ce za ta bai wa sojoji damar yin amfani da duk wani ƙarfin soja, ba tare an riƙa ƙorafin cewa sun take haƙƙin jama’a ba.
“‘Yan bindiga ba su da wani ɓangaren addini da su ka yi riƙo ko ƙabilanci ba. Kawai hatsabibin maɓarnata ne, masu ta’addanci.” Inji Tambuwal.
Haka kuma Tambuwal ya bada shawara cewa gwamnatin tarayya ta hanzarta horas da matasan yankunan da ‘yan bidindiga su ke, domin su riƙa yin aikin samar da tsaro.
Matasan ya kasance Zaratan Tsaron Musamman ne, kuma a horas da su sarrafa makamai, ta yadda za su riƙa tunkarar ‘yan bindiga.
“Bayan an samu nasara, sai a maida waɗannan matasa jami’an tsaron dazuka ta yadda wasu ‘yan bindiga ba za su sake bayyana ba.
“Mu a Sokoto mun haramta ‘yansakai, waɗanda aikin su ya na wuce gona-da-iri, su na kashe waɗanda ba su da wata alaƙa da garkuwa da mutane.
“Irin waɗannan kashe-kashen ne ke harzuƙa ‘yan bindiga zuwa ɗaukar fansa a garuruwan da ‘yansakai su ke.” Inji Tambuwal, wanda ya ce hakan ne kuma ya ƙara ruruta wutar wannan fitina.
Ya ce ya kamata kowa ya sa hannu a taimaki wannan gwamnati domin shawo kan wannan masifa.
Daga nan kuma ya roƙi mutane su riƙa fallasa masu mugun hali a cikin su, ta hanyar gaggauta shaida wa jami’an tsaro.
Discussion about this post