Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya ya fallasa yadda aka karkatar da naira miliyan 113.2 a Ma’aikatar Shari’a, cikin 2019.
Ofishin AGF ya ce an ɗebi kuɗaɗen ne aka ce an biya wasu ayyuka da su, amma tsarin biyan kuɗin ya kauce wa Dokar Kashe Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya.
An zare kuɗaɗen an biya ne ta hanyoyi daban-daban da su ka haɗa da biyan ‘yan kwangila tare da shirya bacar biyan kuɗaɗe ba da sauran hanyoyin da ba su dace ba.
Keta Doka A Ma’aikatar Shari’a:
Tashin farko aka saɗaɗa aka waske da wata naira miliyan 35.8. Amma dabarar da aka yi, sai aka karkasa ta gida 12, a cikin 2019, aka yi wa ma’aikata 12 watandar kuɗaɗen.
Kuɗaɗen dai na manyan ayyuka ne aka kamfata, aka biya ma’aikatan. Sai aka rubuta cewa wai kuɗaɗen tikiti jirgin su ne da lada ko alawus-alawus na tarukan da su ke yi duk wata, sai ladar zuwa taron sanin-makamar-aiki da sauran su.
Akwai ma wani ma’aikatacin da shi kaɗai aka ba shi Naira miliyan 30, ya ci karen sa ba babbaka. Wai ladar zaman taro ta yanar gizo (virtual meeting) a 2019.
Sannan akwai wasu naira miliyan 53.8 su ma da aka karkatas.