Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an samu allurar rigakafin korona har kwalabe miliyan ɗaya, waɗanda lokacin da ya kamata a yi amfani da su ya wuce (expiry date).
Sai dai kuma gwamnati ta ce wa’adin na su ya ƙare ne saboda ba su da tsawon shekarun daɗewa ajiye ba a yi amfani da su ba.
Sanarwar dai Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya sa mata hannu, mai ɗauke da ranar 8 Ga Disamba, ya ce an janye alluran miliyan ɗaya, kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) za ta lalata su.
Sai dai kuma Ministan Lafiya ɗin ya ƙi bayyana adadin yawan kwalaben allurar da kuma sunan kamfanin da ya haɗa ruwan allurar.
Sai dai kuma wata majiya da ke da kusanci da Mai’aikatar Lafiya, ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters, cewa alllurar rigakafin kamfanin AstraZeneca ce (AZN.L), wadda aka shigo da ita Najeriya ta hannun COVAX, bisa jagorancin GAVI mai alaƙa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Yayin da Reuters ta bayyana cewa kwalabe miliyan ɗaya ne, wata majiya da ta san adadin kwalaben ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa yawan waɗanda su ka lalacen ba su kai miliyan ɗaya ba. Amma dai an tabbatar cewa duk a cikin watan Nuwamba ne wa’adin lokacin amfani da su ya wuce.
Reuters ta buga cewa kwalaben rigakafin korona miliyan ɗaya sun lalace a Najeriya, daidai lokacin da ake fama da matsanancin ƙarancin rigakafin ta korona a Afirka baki ɗaya. A ranar Laraba ce kafar yaɗa labaran ta Reuters ta buga wannan labari.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kashi 4 bisa 100 na ‘yan Najeriya miliyan 206 ne kaɗai aka yi wa rigakafin korona.
Wata majiya kuma ta shaida wa wannan jarida cewa yawancin lalatattun kwalaben rigakafin, sun iso Najeriya ne ana sauran makonni huɗu ko biyar wa’adin amfani da su ya wuce. Shi ya sa duk ƙoƙarin da mahukuntan harkokin lafiya su ka yi domin a yi amfani da su kafin wa’adin su ya wuce, ba a samu nasara ba.
Har yanzu dai ana ci gaba da ƙidaya adadin waɗanda lokacin amfani da su ɗin ya wuce.
Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), wadda ita ke da alhakin yi wa jama’a rigakafi, ta shaida wa Reuters cewa har yanzu ana tattara bayanan adadin kwalaben allurar rigakafin da Najeriya ta karɓa. Kuma za a sanar nan da ‘yan kwanaki.
WHO ta ce baya ga waɗanda su ka lalace ɗin, akwai ma wasu kwalaben allurar rigakafi har 800,000 da wa’adin amfani da su zai ƙare cikin Oktoba na watan jiya, amma sai aka yi gaggawar ɗirka wa jama’a allura da su kafin lokacin wucewar amfani da su ɗin ya zo.
Discussion about this post