Wani ɗan ƙabilar Igbo mai suna Simon Odo, ya mutu bayan ya haifi ‘ya’ya sama da 300 daga mata 59 da ya aura.
Asalin Simon Odo ɗan garin Aji ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze, a Jihar Enugu. Ya rasu safiyar Talata bayan ya yi fama da wata gajeriyar rashin lafiya.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan sa mai suna Emeka Odo ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) cewa mahaifin na su ya mutu ya na da shekaru 74.
Emeka ya ce an fara shirye-shiryen rufe gawar mahaifin na sa, wanda ya ce kafin ya mutu ya bar wasiyyar cewa idan ya mutu a gaggauta binne shi, kada a kai gawar sa ɗakin ajiyar gawarwaki. Kuma kada a yi jinkiri wajen binne shi.
“Tabbas mahaifi na wanda aka fi sani da laƙabin Sarkin Shaiɗanu, ƙasurgumin boka ne a yankin mu ya mutu, a ranar Talata. Kuma dama ya shafe makonni uku ya na fama da jiyya.
“Yanzu haka mu na taron iyalan sa ne, domin gaggauta binne shi, kamar yadda ya yi mana wasiyya.”
Emeka ya ce mahaifin sa mutumin kirki ne mai matuƙar kula da dukkan iyalan sa.
Mamacin ya yi suna saboda kiran kan sa da ya ke yi Sarkin Shaiɗanu da kuma yawan ‘ya’yan da ya haifa har fiye da 300.
Sannan kuma a rayuwar sa ya auri mace ɗai-ɗai har 59.