A cikin shekarar 2019, mambobin Majalisar Tarayya sun kashe sama da naira biliyan 5.2, waɗanda aka tsitstsinka a ayyuka daban-daban, kamar yadda wani rahoto ya fallasa.
Waɗannan kashe-kashen kuɗaɗe sun kama daga kuɗaɗen zirga-zirga, gyare-gyare da kula da ayyuka.
Sai dai kuma babu wata hujja cikakkiyar da ke nuni da cewa an kashe kuɗaɗen ta hanyar da ta dace a bisa ƙa’ida a kashe kuɗaɗen.
Haka nan kuma a wani tashin-liƙin, majalisar tarayya sun riƙa biyan albashi na biliyoyin kuɗaɗe wajen biyan haraji, ba tare da wasu takardun da ke nuni da haƙiƙanin an biya kuɗaɗen ga abin da ya cancanta a yi da su ba.
Waɗannan saɓani da bambancin adadin kuɗaɗen da Majalisar Tarayya ta kashe, ya na ƙunshe a cikin rahoton shekara-shekara wanda Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe Na Tarayya (AGF), na 2019.
Majalisar Tarayya, Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyi na daga cikin ɓangarorin da Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗe ya rubuta wa wasiƙun gargaɗi, bisa laifin karya ƙa’idar kashe kuɗaɗe.
An same su kuma da laifi ƙin maida wa CBN kuɗaɗen da ba su kashe ba a ƙarshen kowace shekara. Sannan kuma su na biyan kuɗaɗe ba tare da shiya baca ba.
A cikin rahoton, Babban Mai Binciken Kuɗaɗe ya ce irin wannan ƙin maida wa gwamnatin tarayya kuɗaɗe ya na janyo wa gwamnati maƙudan kuɗaɗe ta hanyar sace kuɗaɗen ko karkatar da su.
A cikin rahoton, ofishin AGF ya ce dukkan ma’aikatun da aka kama da laifin karkatar da kuɗaɗe ko ƙin maida ragowar kuɗaɗen da ba su kashe ba a ƙarshen shekara, babu ko ɗaya da ya maida masa amsar wani bayani ko guda ɗaya.
Kaɗan daga cikin kuɗaɗen da Majalisa ta karkatar a cikin 2019, sun haɗa da naira biliyan 2.55 tsakanin Yuli zuwa Disamba, 2019.
Kuɗaɗen waɗanda aka bai wa majalisa, an ce an kashe su ne shiyya bayan shiyya:
Arewa maso Gabas naira miliyan 187, Kudu maso Kudu, naira miliyan 272, sai Kudu maso Gabas naira miliyan 448.
Arewa ta Tsakiya Naira miliyan 391, Kudu maso Yamma naira miliyan 391, Kudu maso Yamma naira miliyan 629 sai Arewa maso Yamma Naira miliyan 629.
Discussion about this post