Wani lauya Jubril Mohammed ya bayyana cewa tilasta mutane yin allurar rigakafin Korona da gwamnati ta yi bai saba wa dokokin kasa ba.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta umurci duk ma’aikatan gwamnati su je su yi allurar rigakafin cutar korona kafin ranar 1 ga watan Disemba 2021.
Gwamnati ta ce za ta hana ma’aikata shiga wuraren aikin su idan basu da katin shaidan yin allurar rigakafin cutar ko sakamakon gwajin cutar wanda ya nuna cewa basa dauke da cutar.
Mohammed ya ce bisa doka gwamnati na da ikon hana walwala idan cutar ta barke a kasan.
Ya ce gwamnati kan yi haka domin kare kiwon lafiyar mutane da dakile yaduwar cutar.
” Abin da ya kamata gwamnati ta yi shine ta tabbatar mutane sun bada kansu domin gin allurar rigakafin ta hanyar wayar musu da kai musamman yanzu da wani nau’in cutar ya bullo.
“Gwamnati ta bude wuraren yi wa mutane allurar rigakafin sai dai har yanzu mutane kadan ne ke zuwa yin rigakafin.
Sai dai wani lauya dake kare rajin dan Adam Richard Olakulehin ya ce kamata yayi gwamnati ta samar da isassun maganin rigakafi tare da bude isassun wuraren yin allurar rigakafin kafin a tilasta mutane yin allurar rigakafin Korona.
Olakulehin ya ce mafi yawan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake yi wa mutane allurar rigakafin na fama da matsalolin rashin isassun kayan aiki.
Ya ce wadannan matsaloli na cikin dalilan dake hana mutane bada kansu domin yin rigakafin.
Idan ba a manta ba a watan Agusta ne gwamnatin jihar Edo ta Hana ma’aikatan ta shiga wurin aiki ba tare da sun yi allurar rigakafin korona ba.
Hakan da gwamnati ta yi ya sa Charles Osaretin ya kai gwamnati Kara a kotu.
Discussion about this post