Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sunayen mutum 233 da ta kama su da shiga aikin malunta a jihar da takardun bogi wato takardun karya.
Shugaban hukumar SUBEB na jihar Tijjani Abdullahi ya sanar da haka a garin Kaduna ranar Alhamis inda ya kara da cewa gwamnati za ta aika da sunayen su duka kotu domin su fuskanci shari’a kuma a hukunta su.
Ya ce cikin wadanda aka tantance zuwa yanzu, mutum 233 duk sun karya doka ta hanyar shiga aiki da takardun karya a jihar.
” Akwai sauran takardu da ake bincike haryanzu ba a aiko da bayanan sahihancin takardun ba daga jami’o’i da manyan makarantun da ma’aikatan da ake bincike suka saka sun yi karatu a cikin su.