‘Yan bindiga sun sace mutane 20 a kauyukan Kwasare da Chacho dake karamar hukumar Wurno, Jihar Sokoto a ranar Lahadi.
Sirajo Saidu ya bayyana cewa yan uwana 5 aka tafi da su duk a cikin gidan mu. Basu dai kashe kowa ba, yanzu muna jiran su kira mu ne su gaya mana abinda za mu yi.
Shugaban kungiyar Basharu Guyawa ya ce ” A daidai maharan suna barna a Kwasare wasu daga cikin maharan na can kauyen Chacho.
” Muna cikin mawuyacin hali da tsananin tashin hankali, ana kashe mana mutane, ana sace mana mutane , dabbobin mu ba su tsira ba sannan a kusan kullum sai an kai hari kauyukan mu. Abu dai sai dai kawai mu rika cewa Inna-lillahi-wa-inna ilaihir-rajiun. Amma masifar ya kai masifa, muna cikin tashin hankali. ”
Sai dai kuma wani dan jarida Gidan Dare ya ce mutum sama da 20 ne maharan suka sace a kauyukan a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi.
” Ai mutanen da mahara suka sace sun fi mutum 40 a tsakanin ranakun Asabar zuwa lahadi a kauyukan karamar hukumar Wurno.
Jihar Soko to ta shiga bala’in hare-haren yan bindiga babau kakkautawa a wannan lokaci. A cikin makon jiya mahara sun bankawa mota dauuke da mutane sukutum wuta mutane suka mutu.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya roki gwamnati da ta kawo wa mutanen jihar dauki, domin abin ya wuce misali a yanzu.
Ya ce shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kasa kawo karshen wannan hare-hare da ya addabi mutanen jihar.