Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce Sojojin Operation Whirl Stroke a Jihohin Benuwai, Nasarawa da Taraba sun kama baƙin-haure 16 da su ka tsallako daga Jamhuriyar Nijar su na kai hare-hare.
Sanarwar ta ce an kama su a wurare daban-daban cikin jihohin tsakiyar Najeriya.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Tsaron Najeriya Burgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya yi wannan ƙarin haske a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya ke ƙarin haske dangane da nasarorin da dakarun Najeriya ke ci gaba da samu a yankunan ƙasar nan daban-daban.
Ya ce an samu waɗannan nasarorin ne tsakanin ranakun 9 zuwa 23 Ga Disamba.
Ya ce sojoji sun yi gagarimar nasara a Tine-Nune a yankin Mbatin da Tse Yorbee cikin Ƙaramar Hukumar Ukum da Dajin Edumoga a Ƙaramar Hukumar Okookwu a Jihar Benuwai.
An kuma share mahara a Dajin Ugya cikin Ƙaramar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.
Ya ƙara da cewa an kashe ɓatagari 12, kuma an kama wasu baƙin haure su 26.
An kuma ƙwace muggan makamai daga hannun ‘yan bindigar.
A jihar Filato da Bauchi da Kaduna kuma an kama barayin shanu da masu safarar ƙananan yara da ‘yan bindiga da masu fashi da makami.
Discussion about this post