Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana adadin kuɗaɗen albashi da na alawus da kowane ɗan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya ke ɗauka.
Da ya ke jawabi a wurin wani taro kan Ayyukan Majalisa, Lawan ya ce kowane Sanata ya na ɗaukar albashin naira miliyan 1.5 a kowane wata. Shi kuma Ɗan Majalisar Tarayya ya na ɗaukar naira miliyan 1.3 kowane wata.
Ya ce kowane Sanata ana ba shi Naira miliyan 13 domin tafiyar da ayyukan ofis na yau da kullum. Shi kuma Ɗan Majalisar Tarayya ya na karɓar Naira miliyan 8 domin tafiyar da na sa aikin ofis ɗin.
Da ya koma kan Majalisar ɗungurugum, Sanata Lawan ya ce mutane sun fi yi wa majalisa mummunan fahimta da mummunan zato, saboda ita ce ta fi kusanci da su.
A taron wanda Cibiyar NILDS ta shirya, Lawan ya ce “akwai ɓangarorin gwamnati uku. A cikin su Majalisa ce ta farko, saboda ta fi sauran kusanci da jama’a sosai.
“Duk da kowane aikin sa daban, amma wajibin mu ne mu yi aiki tare, domin a samu nasarar komai bai-ɗaya. Saboda nasarar ɗayan mu, nasarar sauran ce. Kasawar ɗayan mu ma kasawar mu ce gaba ɗaya.
“An bijiro da ƙudirori 2,500 ya zuwa 2021. Majalisar Dattawa ke da guda 769, ita kuma Majalisar Tarayya ta gabatar da 1, 634”
Lawan ya ce kusancin da jama’a ke da shi ga ‘yan majalisa shi ya sa mutane ke masu kallon ‘yan amshin Shata. “Amma gaskiyar magana, mu ba ‘yan-amshin-Shata ba ne.”
Discussion about this post