Duk da irin zaman damuwa da halin rashin tsaron da ake fama da shi da kuma tsadar rayuwa a wannan gwamnati, Gwamna Abdullahi Sule ya ce za a yi kewar Shugaba Muhammadu Buhari da mulkin ka bayan ya kammala wa’adin sa ya sauka.
Haka dai ya bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan ganawar da ya je ya yi shi da Buhari, a ranar Talata.
“Na shaida wa Shugaban Ƙasa cewa wasu ayyukan alherin da ya yi, sai bayan ya sauka sannan za a riƙa tunawa ana kewar sa.
daga nan Gwamna Sule ya fara sharara sunayen wasu ayyukan da Shugaba Buhari ya yi, waɗanda ya ce ya kafa muhimmin tarihi wajen samar da ayyukan.
Yawan kashe-kashen da ake yi da yawan garkuwa da mutane, karɓar kuɗaɗen fansa da banka wa gidaje da kayan abincin jama’a wuta da ake yi, waɗannan duk ba su hana Gwamna Sule cewa za a yi kewar mulkin Buhari ba.
Sule ya yi furucin sa amma bai yi magana kan matsalar tsaro da ƙuncin rayuwa wanda komai ya yi tsada sosai a zamanin mulkin Buhari ba.
“Mun tattauna batun samar da gas kuma za kawo ƙwararrun mu daga abin da ya faru da bututun gas na Afrika ta Yamma. Wanda aka jona daga Shagamu ya bi ta Ikeja, kuma dukkan masana’antun da ke wuraren su na amfani da gas ɗin.
“Zuwa yanzu ƙasa kamar Najeriya wadda ke da sama da tiriliyan 200 na kubik ɗin gas a cikin ƙasa, ai babban aiki ne sosai idan aka duba. Amma jama’a ba za su gane haka ba sai bayan Shugaban Ƙasa ya sauka tukunna.”
Ya ƙara da cewa sai ma an fara samar da gas ɗin girke-girke da kuma gas ɗin amfani da motoci wato LNG rukunna sannan za a ƙara fahimtar alherin da ke tattare da gwamnatin Buhari.
Ya ce ya je Fadar Shugaban Ƙasa domin gode masa kan irin goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bayarwa wajen samar da tsaro a Jihar Nasarawa.
Discussion about this post