Ɗaya daga cikin lauyoyin Kanu mai suna Maxwell Opara, ya shaida wa manema labarai a Abuja a ranar Litinin cewa Kanu na neman a ba shi ‘yancin sa na ɗan ƙasa ya samu likitan da ya amincewa ya duba lafiyar sa.
Sannan kuma ya ce wani haƙƙi da aka tauye wa Kanu, shi ne haƙƙin yin ibadar sa ta addinin Yahudu da kuma ‘yancin sauya tufanin da ya ga damar sakawa.
“Mun garzaya kotu ne saboda an hana Kanu ya samu likitocin sa. Sannan kuma an tauye masa ‘yanci. Ya shaida mana cewa jami’an SSS sun gayyaci wasu likitocin da bai yarda da su ba, sun riƙa zuƙar jinin sa har sau 21.
“Idan kun tuna, a can baya Mai Shari’a Zainab Nyako ta Babbar Kotun Tarayya, ta umarci SSS su bar Kanu ya riƙa gudanar da addinin sa na bautar Yahudanci da ya yi imani da shi, amma an tsare shi a keɓantaccen wuri, an hana shi yin ibada.
“Sannan kuma Zainab ta umarce su su bar shi ya riƙa sauya tufafi a lokacin da ya ke so, kuma irin waɗanda ya ga damar sakawa, amma sun hana shi.”
Ana tsare da Nnamdi Kanu tun cikin watan Yuni, bayan da aka cumuimuyo shi daga ƙasar Kenya.
Bayan kawo shi Najeriya ne aka tsare shi a Hedikwatar SSS a Abuja, har yau kuma ya na can.
An kamo shi ne bayan ya tsallake beli ya arce daga Najeriya zuwa Birtaniya.
Cikin ƙarar da ya shigar, lauyan Kanu ya nemi a bar shi ya yi addinin sa, a bar shi ya nemi likitocin da ya amince da su. Sannan kuma a bar shi ya riƙa canja tufafin da ya ke da ra’ayin sanyawa.