Babbar Kotun Abuja ta ƙara jaddada cewa Haruna Ɗanzago na ɓangaren APC ɗin su Sanata Shekarau ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano.
Hakan ya biyo ƙarar da ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar, wanda ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, a zaɓen da ɓangaren Shekarau su ka shaida wa kotu cewa ba a shigar da mabiyan su a ciki ba.
Ɓangarorin biyu sun yi zaɓe daban-daban a rana rana ɗaya, tun daga ƙananan hukumomi har zuwa shugabanni na jiha.
Bayan ɓangaren Shekarau ya yi nasara a kotu, ɓangaren Ganduje ya sake garzayawa kotun ya nemi ta jingine hukuncin halasta Ɗanzago a matsayin Shugaban APC a Kano da ta yi.
Sai dai kuma Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya sake jaddada hukuncin da ya zartas tun a ranar 30 Ga Nuwamba, cewa Ɗanzago ne halastaccen shugaba. Kuma tun daga ƙananan hukumomi har jiha, jam’iyya na hannun su.
Haka nan kuma kotu ta ci tarar su Abdullahi Abbas naira miliyan 1, waɗanda ta ce su biya Haruna Ɗanzago, saboda sun ɓata masa lokaci.
Dama tun da farko sai da kotu ta gargaɗe su cewa kada su sake su sake wani zaɓe kuma.
Bibiyar Tirka-tirkar Rikicin Da Ya Ci Abdullahi Abbas Da Yaƙi: