Fadar Shugaban Ƙasa ta maida martani ga jaridar Daily Trust, dsngane da wani kakkausan Ra’ayin Jarida, wanda ta buga mai ɗauke ya zafafawa kan Shugaba Muhammadu Buhari bisa abin da ta kira “Rayukan ‘Yan Arewa Ba Shi Wata Daraja A Gwamnatin Buhari.”
A cikin rubutun, Daily Trust ta yi wa Buhari tatas, tare da fitowa ɓaro-ɓaro ta bayyana cewa ya kasa kare rayukan al’ummar Najeriya, musamman yankin Arewa, mazaɓar da ya fito.
Jaridar bayan ta zayyana irin kashe-kashen da ake fama da su a kwanan nan, ta kuma yi waiwaye baya kafin Buhari ya hau mulki, inda ta tunatar da shi cewa a lokacin gwamnatin baya ya riƙa fitowa ya na ɓaɓatun cewa an kasa kare rayukan jama’a.
Premium Times ta sha buga labaran irin mawuyacin halin ƙuncin da al’ummar jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kaduna da Neja ke ciki. Ire-iren waɗannan kashe-kashen ne da garkuwa da mutane ana karɓar kuɗin fansa ya sa Daily Trust ta fito a karon farko ta ce rayukan ‘yan Najeriya ba su da wata daraja a ƙarƙashin gwamnatin Buhari.
Har ila yau, jaridar ta bada misali cike da damuwa ganin yadda Buhari ke yin ko-in-kula wajen kai ziyarar ƙarfafa wa talakawa guiwa, waɗanda su ne dai su ka sadaukar da rayuka da dukiyoyin su wajen zaɓen Buhari.
A ɗaya gefen, Trust ta ragargaji Buhari saboda garzayawa bikin zagayowar ranar haihuwar Bisi Akande a Legas, a yankin Arewa da ake kashe-kashe kuma, sai ya tura wakilci.
“Jama’a mu na gabatar maku da Arewacin Najeriya, yankin da rayuwar jama’ar sa ba ta da wata daraja a ƙarƙashin mulkin Buhari. Jama’ar da su ka fito dafifi su ka zaɓe shi sau biyar a tsawon shekarun da ya shafe ya na haƙilon sai ya zama shugaban ƙasa.”
Sai dai kuma a martanin da Fadar Shugaban Ƙasa ta maida wa Trust, Mai ɗauke da sa hannun Garba Shehu, Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, ya bayyana kakkausan rubutun da Trui ta yi cewa akwai rashin adalci a cikinsu.
Garba Shehu ya yi bayanin irin ƙoƙarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an magance matsalar tsaro. Sannan kuma ya bayyana yadda lamarin ba tun yau ya zama murɗaɗɗe ba.
Haka kuma ya tunatar cewa matsalar ‘yan bindiga ta zama ruwan-dare a Afrika ta Yamma, musamman daga Burkina Fasso, Mali, Nijar da wasu ƙasashen da daga can guguwar bala’in ta bugo zuwa Arewacin Najeriya.
Shehu ya yarda akwai matsalolin, amma kuma ya nuna yadda ake ƙoƙarin kawar da su, kamar yadda ya ce an kusa cin ƙarfin Boko Haram.
Discussion about this post