Bisa ga rahotannin da gidajen jaridu suka wallafa a makon jiya, wato daga litinin zuwa a Asabar sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 63 a kasar nan a tsawon waɗannan kwanaki.
Rahotannin sun nuna cewa an samu karin kashi 200% kan yawan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a daga makon jiya zuwa karshen wannan makon.
A makon jiya ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama, ciki harda matafiya 37 da mahara suka cinna wa motar su wuta suka babbake.
Rahotannin sun kuma nuna cewa ‘yan bindigan sun kashe jami’an tsaro 12 a cikin makon jiya amma a jami’i ɗaya aka kashe a cikin makon da ya gabata.
Arewa maso Yamma
A rikicin da aka yi tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Kirikasamma dake jihar Jigawa mutum uku suka gamu da ajalinsu.
Wani mazaunin garin Sunusi Doro ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati ta aika da jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya a karamar hukumar.
Daga nan a karamar hukumar Sabon Birni jihar Sokoto ‘yan bindiga sun cinna wa motar matafiya da suka taso daga jihar zuwa jihar Kaduna wuta inda a ciki mutum 37 suka mutu.
Wani da abin ya auku a idonsa ya bayyana wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigan sun far wa matafiyan da safe karfe 9 ranar Litini.
‘Yan bindiga sun kashe mutum bakwai sannan sun banka wa motoci da abinci wuta a hanyar Shinkafi zuwa Moriki.
Wani mazaunin yankin Musa Shuaibu ya ce maharan sun tare akalla motoci 15 a wannan hanya sannan sun cina wa biyar daga ciki wuta.
Bayan haka ‘yan bindiga sun kashe kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Katsina Rabe Nasir.
‘Yan bindigan sun kashe Nasir a gidan da ranar Alhamis da yamma.
Sannan tsakanin ranar Juma’a da Asabar ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu sannan sun yi garkuwa da mutane da dama daga wasu kauyukan karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto.
Arewa ta Tsakiya
‘Yan bindiga sun kashe wani babban Malami dake koyar da darasin harkokin kasuwanci a kwalejin koyar da kimiya da fasaha na jihar Benue dake Ugbokolo, Echobu Adah.
Maharan sun kashe Adah a hanyar Eke Olengbecho zuwa Olayenga dake karamar hukumar Okpokwu.
Wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wata matar aure mai suna Salamatu a kauyen Piri dake gundumar Kwali a Abuja.
An kuma yi garkuwa da mutum 8 tsakanin ranar Talata da Laraba.
A ranar Laraba ‘yan bindiga sun kashe mutum tara a kauyen Ba’are dake karamar hukumar Mashegu jihar Neja.
Kudu maso Kudu
Wani magidanci mai suna Ikrdi Peter ya kashe kansa bayan ya kashe matarsa.
Jami’an tsaro sun ce basu da tabbacin dalilin da ya sa Peter ya kashe matarsa amma wani makwabcin su ya ce Peter ya fada rijiya bayan ya kashe matarsa.
Kudu maso Yamma
‘Yan bindiga sun kashe jami’in hukumar FRSC Omiwoye Sunday a jihar Ondo.
Maharan sun kashe Sunday a kofar gidan abokinsa yayin da yark kokarin hana mahara kai wa wasu mutane hari.
Discussion about this post