Jami’an Tsaron Najeriya sun kashe sama da mutum 13,000 tsakanin 2011 zuwa 2021, kamar yadda sabon rahoton da Ƙungiyar CDD ta wallafa.
Premium Times ta samu wannan rahoton a ranar Litinin, wanda cibiyar ta bi diddigin kashe-kashen take haƙƙin jama’a da jami’an tsaro su ka yi a cikin shekaru 20.
Da CDD ke bayyana yadda aka riƙa take haƙƙin jama’a a zamanin sojoji, ta ce “sojoji sun riƙa take ‘yancin jama’a tsawon shekaru 16.”
Daga nan kuma rahoton ya bi yadda aka riƙa kashe-kashen take haƙƙin jama’a tsakanin 1999 bayan komawa mulkin dimokraɗiyya zuwa baya-bayan nan.
Ma’aunai 4 Da CDD Ta Auna Take Haƙƙin Jama’a Da Su:
Ma’aunin farko shi ne tsarewa ko kulle mutum ba a bisa yadda doka ta gindaya ba. Sai azabtar da mutum da kuma kisa ba tare da hukuncin kotu ba. Daga nan kuma sai ma’auni na huɗu, wanda ya ƙunshi tauye haƙƙin faɗin ra’ayi, hana mutane shirya taruka da kuma danne ‘yancin jan jarida.
CDD ta ce waɗanda ta lissafa a sama “duk aikin sojojin Najeriya ne.”
Rahoton ya ce azabtarwa da kisa ba tare da umarnin kotu ba, ya yi muni sosai a Najeriya tun daga 1999, “kuma akasarin kisan duk jami’an tsaro ne su ka aikata shi.”
Rahoton ya ce gwamnatoci ɗaya bayan ɗaya sun riƙa yin amfani kisa ba bisa ƙa’ida ba wajen murƙushe zanga-zangar masu neman ɓallewa da kuma masu aikata ta’addanci.
“Kisa ba bisa ka’ida ba da jami’an tsaro su ka riƙa yi a cikin shekaru 10, ya yi sanadiyyar rasa rayuka 13,241 a Najeriya, tun daga 2011 zuwa yanzu.”
CDD ta bada misali da batun Sambo Dasuƙi, inda ta ce Gwamnatin Najeriya ta take umarnin kotu, ciki har da wanda Kotun ECOWAS ta bayar cewa a sake shi, a ranar 4 Ga Oktoba, 2016.”
“Sannan kuma a cikin gidajen kurkuku ana take haƙƙin jama’a sosai a Najeriya, inda a cikin shekaru 10 da su ka gabata ake cusa ɗaurarru a ƙuntataccen ɗaki.
“Ana tsare mutane su nunka yawan waɗanda ya kamata su riƙa kwana a ɗaki ɗaya sau kashi 1000 ba ma sai kashi 100 ba.”
Rahoton CDD ya yi raga-raga da ‘yan sandan SARS, waɗanda ya ce “sun shahara wajen azabtar da ɗan adam irin azabtawar da ko dabba bai kamata a yi masa haka ba. Su na gallaza wa ɗan adam domin neman wani bayani daga bakin sa, ko kuma a matsayin horo.”
“Tsakanin Janairu 2017 zuwa Mayu 2020, Amnesty International ta buga rahoton azabtarwa daga SARS kan mutum 82 da aka kashe ta hanyar ratayewa, dulmiyawa cikin ruwa da kisa.
“A lokacin kullen korona kuwa an bayar da rahoton take haƙƙin jama’a sau 105 a Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a. Akasari wannan kuma duk ‘yan sanda ne su ka aikata su.”
Discussion about this post