Rahoton da ƙungiyar Tantance Wadatar Irin Shuka Ga Manoman Afrika (TASAI), ya bayyana cewa Najeriya ce ƙasar da ke da ƙarancin jami’an horas da manoma a cikin 2020, a fadin kasashen Afrika baki ɗaya.
TASAI (African Seed Access Index) ya bayyana cewa ƙasar Ruwanda ce ta farko wajen yin na ɗaya a matsayin ƙasar da ta fi sauran ƙasashen Afrika watadar jami’an horas da manoma dabarun noma.
Rahoto ya ce daga Rwanda sai Zimbabwe ce ta biyu, sai Burkina Faso ta zo ta uku, Zambiya ta huɗu, iya kuma Mali ta biyar.
Najeriya ce ta ƙarshe a can ƙasan jerin sunayen, ita da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, Uganda da kuma Kenya.
Matsayin Najeriya a ƙarancin yawan jami’an horas da manoma dabarun inganta noma a cikin 2019 shi ma a can ƙarshe ta ke, kuma dama a shekarun baya, 2017 da 2018 duk ba ta canja zani ba.
Najeriya ta yi ta ƙoƙarin bunƙasa harkoki noma domin rage dogaro da ribar ɗanyen mai.
Ciki watan Maris, 2021, gwamnatin Najeriya ta ƙara ɗauki hayar jami’an horas da dabarun noma su 75,000, domin a ƙara bunƙasa fannin noma da samar da wadataccen abinci.
Ma’aikatar Harkokin Gona a cikin 2019 ta ce akwai jami’an horas da dabarun noma da ta ɗauka haya, har su 14,000. Daga cikin su guda 6,000 daga cikin su ma’aikatan gwamnati ne, sauran guda 8,000 kuma hayar su aka ɗauka, duk masu zaman kan su ne.
Rahoton da jaridar Vanguard ta buga ya nuna cewa gwamnati ta ce an samu ƙarancin jami’an horas da manoma dabarun noma ne saboda tsarin ya samu koma-baya tsawon shekarun nan da su ka gabata.
Dalili, inji gwamnati shi ne saboda rage kuɗaɗen da ake kashewa a fannin noma da aka yi, sai kuma sauye-sauyen tsare-tsaren harkokin noma da raguwar ma’aikatan harkokin noma, saboda matasa da dama ba su nuna sha’awar tsunduma cikin sana’ar kasuwancin noma.
An buga rahoton TASAI a cikin Oktoba, kuma ya nuna ƙarancin jami’an horas da manoma dabarun noma, musamman fannin amfani da irin shuka ga ƙananan manoma a faɗin ƙasar nan.