A ranar Alhamis ne Rashidat Ogunniyi mai shekara 40 ta roki kotun dake Igando a jihar Legas ta raba auren ta na shekara 12 saboda mijinta Kazeem ya fi daraja karen gidan su fiye da ita.
Rashidat ta ce tun da ta auri Kazeem kwanciyar hankali yakare mata kwatakwata.
Haka kawai idan Kazeem ya bushi iska sa ya rika jibga ta akan abinda bai taka kara ya karya saboda kawai son zuciya.
“Akwai ranar da yayi min dukan tsiya a bainar jama’a ya yayyaga min kaya kuma bai yi ko nadama.
“Kazeem ya kwaso kayan sawa ta ai kona wata rana, in banda baki da limamin masallacin unguwan mu ya saka ba ya hanashi da shi kenana sai dai in nemi wasu kayan ba wadanda nake da su ba.
Ta roki kotu ta raba auren sannan ta bata izinin rike ya’yan su.
A karshe dai alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya dage shari’ar zuwa ranar 18 ga Janairu.