Tun bayan da kamfanin Meta (tsohuwar kamfanin Facebook) a 2012 ta sayi Instagram, dandalin wallafa hotuna da bidiyo dan sada zumunta, wanda Kevin Systrom da Mike Krieger suka kirkiro, ya kasance wani dandalin raba bayanai masu mahimmancin gaske.
A duniyar kafofin sadarwa na dijital da ke sauyawa, aikin Instagram ba kasancewa wurinn da masu neman nishadi ke zuwa nuna salon rayuwansu ne kadai ba, yana kuma kasancewa gadan da ke tsakain masu amfani da soshiyal mediya da wadanda ke labarai a al’ummar kasa da kasa.
Masu amfani da soshiyal media, a rukunnan shekarun haihuwa daban-daban sna ganin cewa dandalin mai mutane sama da billiyan daya da digo na da saukin sha’ani saboda yanayin hotuna da salon da ake amfani da shi wajen raba bayanai.
Yanzu da ya kaddamar da manufar samun kudi Instagram ya zama babban wurin samun kudi inda mutane suna iya sayar da bidiyo su sami kudaden shiga a abin da za’a iya amfani da shi a madadin YouTube, mallakar google.
Bunkasar Instagram
Tun shekarar 2019, Instagram ta ke habbaka, musamman tsakanin matasa wadanda ke dogaro da manhajan wajen samun karin bayani dangane da labaran da ake bayarwa “cin sauki, a takaici kuma da hotuna masu kayatarwa.”
Wani bayanin da kamfanin dillancin labaran Reuters ya wallafa kwanan nan mai taken “kewaye ‘annobar yawan bayanai’: Yadda mutane a kasashe shida suke samu da kimanta labarai da bayanai dangane da coronavirus” ya bayyana yawan sha’awan da aka samu kan Instagram da sunan da ya yi tsakanin masu amfani da yanar gizo.
Binciken da aka yi a 2020 domin rubuta yadda mutane a wasu kasashen ke amfani da bayanan da suka samu dangane da COVID-19 daga farkon zuwan annobar ya nuna cewa “matasa sun fi dogaro da sabbin kafafe, masu amfani da hotuna irinsu Instagram… dan samun bayanai” dangane da kwayar cutar. Wannan hoton na kasa, na nuna manhajoji da yawan matasa tsakanin shekaru 18-24 da suka yi amfani da su dan labaran coronavirus a makon da ya gabata
A nazarin da yayi mai taken “Instagram zai wuce Tiwita a matsayin majiyar labarai,” editan BBC Media Amol Rajan ya ce bunkasar Instagram a matsayin majiyar labarai abin yabawa ne.
Yayin da yake danganta ra’ayin shi da rahoton cibiyar kamfanin dillancin labaran Reuuters, dan jaridan kuma mai karanto labarai ya sake yin hasashen cewa ba da dadewa ba Instagram zai fara kama da ra’ayin jama’a wanda kuma zai baiwa kafofin yada labarai zabin da ba za su iya gujewa ba daga nan sai ya tsere wa Tiwita wanda a yanzu ‘yan jarida suka fi amincewa da shi.
Wani dalili mai mahimmanci wajen bunkasar Instagram da yadda yake samun karbuwa a matsayin majiya ta bayanai shi ne yadda manyan kamfanonin labaran da ke da kima a idon jama’a ke zuwa wurin suna amfani da shi wajen baiwa mabiya shafukan su labarai.
Abun mamaki ne yada kusan kowace kafar yada labaran da aka sanu irin su BBC, Aljazeera, Reuters, Punch da sauransu yanzu dk suna da shafuka a Instagram. Inda suke hada bayanai kan salon rayuwa da kabarai tsantsa. Sa’annan akan sarrafa bayanan biyu da kyau a yi amfani da hotunan ta yadda suke janhakalin ma’abota shafin.
Hasali ma mutane sun fi son bin labarai a shafin saboda dandalin na bayar da damar sanya labarai ta yadda mai sha’awa ba sai ya je babban shafinsu kafin ya karanta cikakkne labarin ba.
A shekarar 2020 dalibai hudu daga jami’o’i daban-daban a Afirka ta Kudu: Christina Gumpo, Tinashe Chuchu, Eugine Maziriri and Nkosivile Welcome Madinga sun gudanar da bincike dangane da irin karbuwar da shafin Instagram ke samu tsakanin matasa wadanda ke neman wuraren zuwa hutu.
A rahoton da suka rubuta mai taken “Nazarin yadda ake amfani da Instagram a matsayin wajen samun bayanai ma matasa wadanda ke neman wuraren zuwa yawon bude ido,” daluban sun ce akwai alaka sosai tsakanin “dabi’ar amfani da Instagram wajen zaban wuraren zuwa yawon bude ido da niyyan amfani da shi wajen gano wuraren zuwa bude ido.”
Sun ce dandalin mai amfani da hotuna da bidiyo “yana kalubalantar tunanin kaga abubuwan wadanda ke da ruwa da tsaki a fanin yawon bude ido wajen tallata wuraren zuwa yawon bude ido a duniya.” Wannan na nufin shafin ya zama mai ruwa da tsaki wajen kawo bayanai da kuma tasiri a kan ra’ayoyin mutane.
Matsalar Instagram
To sai dai matsalar Instagram ita ce tana bukatar hotuna sosai in ji Jennifer Grygiel wata farfesa ta sadarwa.
Malamar da ke koyarwa a jami’ar Syracuse ta kuma ce a ra’ayinta “mutane suna sanya hotunan abubuwa (na ban dariya ko barkwanci) da niyyar sauya ra’ayin jama’a ba lallai dan su karu da shi ba kuma mutane na bukatar …
Wani abu mai dauke da sarkakiyakuma shi ne yadda kowa ma zai iya zama mai daukan labarai ko kuma dan jarida, abin da ke janyo damuwa dangane da sahihancin labaran.
Haka nan kuma, ba wuya an yaudari jama’a kan wani mashahurin ra’ayi. Labaran karya na fake news da yaudara suna saurin yaduwa a wannan dandalin. Wannan haka ne saboda taurarin fim da mawaka da influencers wadanda ke yawan amfani da dandalin suna tasiri sosai kan ra’ayin jama’a wanda wata sa’a yak e batar da su musamman a mahimman batutuwa.
Kwanan na ne wata mai wakar rap haihuwan kasar Trinidad, Nicki Minaj mai ma’abota milliyan 163 a Instagram ta yi zargin cewa allurar COVID-19 ya yi sanadiyyar “kumburin gwaiwa” abin da ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya. Dan haka a yi tunanin irin hadarin da masu yawo da labaran karya na fake news za su iya kawowa.
Discussion about this post