Wasu mutane masu kwana a gaba, sun tsere daga sansanin yaran gogarman ‘yan bindiga Bello Turji, bayan sun shafe kwanaki a hannun maharan.
Waɗanda su ka kuɓuta ɗin dai sun tsere ne daga sansanin ‘yan bindiga da ke cikin Dajin Suruddubu da ke Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto, ranar Asabar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Isa, Abubakar Yusuf, ya shaida wa PREMIUM TIMES a hirar da ta yi da shi ta wayar tarho cewa, yanzu haka kuɓutattun su na Babban Asibitin Isa.
Sannan kuma ya ce, “mutum 8 ‘yan asalin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ce, a nan Jihar Sokoto. Su kuma uku daga nan Ƙaramar Hukumar Isa ne. Sai uku kuma daga Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda cikin jihar Zamfara.
Yusuf ya ce mutanen sun samu nasarar arewa ne a lokacin da maharan su ka fita kar farmaki a wasu ƙauyuka.
Wannan jarida ta buga labarin yadda ‘yan bindiga sun sun kwashi mutane a garuruwa 5, sun yi kisa, kuma sun sace Limamin Gatawa.
Yanzu haka dai Babban Limanin Gatawa na Masallacin Izala da ke cikin yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, ya na hannun ‘yan bindiga.
Mahara sun yi gaba da Liman Aminu Garba a ranar Juma’a, inda su ka dira masallacin, su ka hana shi jan Sallah, su ka yi gaba da shi.
An kai wannan hari ne kwana ɗaya kafin isar tawagar da Shugaba Muhammadu Buhari isa Sokoto domin isar da saƙon tabbatar da tsaron al’ummar jihar daga bakin Shugaban Ƙasa.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa washegari kuma a ranar da tawagar ta bar Sokoto, mahara sun koma Gatawa sun saci mutum uku.
Buhari ya sha ɗaukar alƙawarin kare rayukan jama’a, amma abin ya zama tamkar tatsuniya.
Basharu Guyawa, wani jagoran Rundunar Adalci kuma ɗan yankin Sabon Birni, ya shaida wa wakilin mu cewa, “yan bindiga sun tafi da Liman Aminu Garba na Masallacin Izala na Gatawa, bayan sun hana shi yin jam’i, a lokacin da suka ritsa shi.
“Har zuwa yanzu ɗin nan babu labarin inda ake tsare da shi, domin ba su kira ba, ballantana a ji daga bakin su.
“Sun dawo ranar Asabar, su ka sake tafiya da mutum uku. Daga baya su ka sako ɗaya ya koma gida. Da za su sake shi, su ka ba shi lambar waya da za a kira su domin a kai kuɗin fansa. Har ma su ka faɗi inda za a kai kuɗin, a haɗu a can a ba su.”
A ranar Asabar ɗin ce kuma su ka shiga garin Maɗaci su ka kashe mutum biyu.
Wani mai suna Ɗanmalam ya ce wa wakilin mu, “wallahi ni ma Allah ya sa ina da sauran kwana a gaba. Saboda da na ji rugugin bindigogi, sai na yi sauri na shige cikin rumbu.
“Allah ya taimake ni ba su bincika cikin rumbun ba. Saboda sun tsaya bincike gida-gida, ɗaki-ɗaki su ka riƙa bincike.’
Guyawa ya tabbatar da cewa tsakanin Juma’a zuwa Asabar, mahara sun tare hanyar Sabon Birni zuwa Gayawa. Sannan sun kwashi mutane a Maɗaci, Lugu, Bargaja, Ɗanzake da Gazau.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Sokoto Sanusi Abubakar ya ce wa wakilin mu zai tuntuɓe shi daga baya.