Gwamnan jihar Kaduna ya amince a yi wa ma’aikatan jihar Karin kudi a alabshin su, kyautar Disamba kowa ya je ya sha lagwada.
Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya sanar da haka ranar Talata a Kaduna
Muyiwa ya ce a bisa ga tsarin, za a biya ma’aikata daga mataki 1-7 karin kashi 100 na albashin su cif, daga mataki na 8-13 kuma kashi 40 cikin 100 na albashin su sai kuma manya daga mataki 14 zuwa sama kashi 30 cikin 100 na albashin su.
Gwamnatin Kaduna za ta kashe naira biliyan N1.382 domin biyan ma’aikata wannan garabasa.
PREMIUM TIMES HAUSA sun tattauna da wasu daga cikin ma’aikatan jihar inda suka yaba wa gwamnatin jiharkan wannan abu da ta yi.
Hadiza Nasiru, Malamar makaranta ta ce wannan kokari na gwamnati zai taimakawa mutane matuka musamman a wannan lokaci na bukuwan kirsimeti da sabuwar shekara da aka tunkara.
” Kayan abinci sun yi matukar tsada. wannan kudi da gwamna zai bamu zai taimaka matuka a wanna lokaci. Muna godiya.
Discussion about this post