Tsohon Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya, Air Chief Marshall Mohammed Umar Dikko, ya bayyana wa kotu cewa shi bai saci kuɗaɗen Hukumar Sojojin Saman Najeriya ba, kamar yadda EFCC ta yi zargin sa.
Umar ya shaida wa kotu cewa ya tara kuɗaɗen da ya sayi kadarorin sa ne daga kyaututtuka kan da shugabannin ƙasashen Afrika su ka riƙa ba shi, sai kuma kuɗaɗen guzurin da gwamnatin Najeriya ta riƙa ba shi a duk lokacin da zai yi tafiya zuwa ƙasashen waje.
A ranar Laraba ce Dikko ya shaida wa Mai Shari’a Nnamdi Dimgba cewa, ya shafe shekaru 35 ya na aikin sojan sama, kuma a lokacin ya samu dama mai yawa ta kyaututtuka a rayuwar sa.
A lokacin da ya ke amsa tambayoyin lauyan EFCC, Sylvanus Tahir, Dikko ya ce:
“Ina so Mai Shari’a ya sani cewa a shekaru 35 da na shafe ina aikin sojan sama, na daɗe ina tuƙa jiragen Shugaban Ƙasa, kuma babu shugaban ƙasar Afrika wanda ban tuƙa ba, sai na Cote D’ivoire da Gabon kaɗai.
“Ta wannan dalili na samu kyaututtuka da dama a hannun su. Sannan kuma daga nan Najeriya na je kwasa-kwasai da dama ƙasashen waje. Kuma duk lokacin da zan fita da jirgi daga ƙasar nan ko wata ƙasa, ana ba shi sallama ta mai kauri a matsayin kuɗin guzuri.”
Dikko wanda ya shugabanci sojojin sama a lokacin Jonathan daga 2010 zuwa 2012, tun da farko dai EFCC tuhuma bakwai ta ke yi masa a kotu. Amma Mai Shari’a Dimgba ya yi watsi da tuhuma shida saboda rashin gamsasshiyar hujja.
A yanzu dai ana tuhumar sa ne da wawurar naira miliyan 66 kacal.
“Na kasance tun tashi na ni ƙasaitaccen manomi ne. Ina da fankamemiyar gona a Abuja mai faɗin hekta 17 a Abuja. Kuma akwai ma wata. A Kaduna ina da gona mai faɗin hekta 4 da mai faɗin hekta 200.” Inji Dikko.
Wancan caji na farko guda shida dai an zarge shi da mallakar gidaje biyu a Abuja, ɗaya a Kano sai kuma biyu a Kaduna.
Za a ci gaba da shari’ar a cikin Disamba.