Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa cutar korona samfurin Omicron ta yadu zuwa kasashe 23 a yankuna biyar daga cikin shida dake karkashin Ikon hukumar WHO.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka wa manema labarai a Geneva a cikin makon jiya.
Ya ce bisa ga yadda cutar ke yaduwa kungiyar na hasashen cewa za a samu karuwar yawa-yawan mutanen da suka kamu da cutar akwana a tashi.
WHO ta ce akwai yiwuwar cewa samfurin Omicron na da karfin kariyan da ake samu daga cikin maganin rigakafi sannan cutar na da saurin yaduwa.
Sai dai Ghebreyesus ya ce babu Wanda ke da tabbacin haka domin har yanzu ana yin gudanar da bincike akan cutar.
Shugaban WHO ya yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali wajen daukan matakan da za su daike yaduwar cutar amma ba hana matafiya shigowa kasashen su ba.
Ya ce yi wa mutane allurar rigakafi da yi wa mutane gwajin cutar, killace matafiya na daga cikin hanyoyin da zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
” Yin amfani da matakan da aka yaki dasu wajen rage yaduwar Korona Samfurin Delta zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
WHO ta ce bisa ga alkaluman yaduwar cutar korona sumfurin Delta da aka fitar ya nuna ce mutum miliyan 261 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum miliyan 5.2 a duniya.
Ghebreyesus ya ce ranar daya ga Maris 2022 WHO za ta zauna da kasashe 194 dake karkashin inuwar kungiyar domin tattauna matakan da za su taimaka wajen. Dakile yaduwar cutar sumfurin Omicron.