Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 49 ne ke dauke da kwayoyin cutar korona samfurin Omicron a Najeriya zuwa yanzu.
Manajan kula da shashen yaɗuwar cututtuka na Hukumar NCDC, Luka Lawal, ne ya sanar haka a taron da ya yi da manema labarai a Abuja.
Lawal ya ce daga ranar Litini Najeriya ta zama ƙasa ta uku a jerin kasashen Afrika da samfurin Omicron ta fi yawa baya ga kasashen Afrika ta Kudu dake da mutum 1,296 da Botswana dake da mutum 291.
Bayyanar Korona samfurin Omicron
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga Disambar 2021 Najeriya ta shiga jerin kasashen duniya da samfurin Omicron ta bayyana.
Cutar ta fara bullowa a kasar Afrika ta Kudu inda bayan haka kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa cutar ya zama abin damuwa.
A Najeriya hukumar NCDC ta fara gano cutar a jikin wasu matafiya baki da suka shigo Najeriya daga Afrika ta Kudu.
Daga baya hukumar ta ce cutar ta ci gaba da yaduwa a kasar nan.
Zuwa yanzu samfurin Delta ce ta fi yaduwa a Najeriya inda a ranar 20 ga Disambar 2021 mutum 2,237 suke ɗauke da ita.
Cutar Korona a Najeriya
Bisa ga alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutum 233,353 sannan mutum 2,991 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
A ranar Laraba adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya karu daga 12,547 zuwa 16,569.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum 3,751,696 gwajin cutar a Najeriya.