Ƙungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnonin Arewa saboda abin da ta kira cewa sun nuna rashin tausayi ga al’ummar yankunan karkarar da ‘yan bindiga ke kashewa da sacewa a Arewa.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Emmanual Yawe ya fitar a Kaduna, a ranar Litinin, ya ce shugaban da gwamnonin kwata-kwata ba su tausayawa ko yin alhinin ɗimbin mutanen da ake kashewa a Arewa.
ACF ta nuna cewa Buhari da Gwamnonin Arewa ba su maida hankali ga komai ba, sai kan rayuwar kan su da ta iyalan su kawai.
“Shugaban Ƙasa da Gwamnonin Arewa sun nuna cewa rayuwar su da rayuwar ‘ya’yan su da matan su ce kawai su ka damu da ita, sai fa ta ofishin da su ke kan mulki.
“In banda Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, babu wani shugaba ko gwamna ɗaya da ke garzayawa jajen gani da ido idan Boko Haram sun kai wa talakawa hare-hare.
“ACF na mai kira da jaddadawa da babbar murya cewa bai yiwuwa a zuba ido ana ganin yadda ake kashe bayin Allah, waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba a Arewacin Najeriya.
“Kisan baya-bayan nan shi ne wanda aka kashe mutum 38 yankin garuruwan da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Giwa cikin Jihar Kaduna.
“Amma duk wannan kisa da ake yi, bai sa Shugaba Buhari tsallakewa ya tafi taron Baje-koli a ƙasar Turkiyya.”
Cikin makonni biyu dai an kashe mutum 101 a jihohin da ake fama da wannan kashe-kashe.
Buhari ya harzuƙa ‘yan Arewa, musamman ganin yadda aka sha shagalin bikin naɗin ɗan sa Yusuf Buhari a sarautar Talban Daura, Hakimin Kassarawa a Jihar Katsina.
Discussion about this post